Saboda gujema saki, matan aure a Borno sun dukufa wurin koyon girke-girke

Saboda gujema saki, matan aure a Borno sun dukufa wurin koyon girke-girke

Aure da yawa na mutuwa a sanadiyar rashin iya girki mai dandano da zai iya janyo hankali mazaje. Wannan wani bincike ne da Aisha Musa Kidah tayi a birnin Maiduguri.

Wannan dalilin ne ya sanya Aisha ta bude wata makarantar koyar da girke-girke masu tafiya da zamani kuma wadanda kan iya sa mazajen aure su dauke idonsu daga wani abincin na waje. Makarantar na koyawa matan aure da kuma ‘yan mata wadanda suka kai munzalin aure girki.

KU KARANTA:Kisan ‘yan sanda: An kama sojoji da ‘yan sanda sama da mutum 25

Sunan makarantar Na’ish Kitchen, kuma an bude makarantar ne a watan Janairun shekarar 2019, a yanzu haka makarantar da horar da mata 100 wadanda akasarinu matan aure ne dake zaune a Jihar Borno.

Har wa yau, akwai wasu mata 20 dake koyon girke-girke a makarantar ta Na’ish yanzu haka. Koyar da matan aure da kuma ‘yan mata shi ne jigon kafa wannan makarantar amma duk da wannan akwai zaurawan da rikicin Boko Haram ya shafa wadanda ke amfana da makarantar.

Na’ish kitchen ya horar da zaurawa 200 wadanda mazajensu suka rasa rayuwarsu a fagen fafatawa da kungiyar Boko Haram.

Shirin koyar da girke-girke ga musamman zaurawan jami’an tsaro ya samu wata kulawa ne ta musamman daga wata kungiya mai zaman kanta mai suna Creative.

Ga abinda Aisha ta fada dangane da makarantar: “ A watan Janairun 2019 na bude wannan makarantar kuma na kashe kimanin miliyan N3 wurin sayen kayan da muke aiki da su.

“ Muna koyar da girke-girke irin namu na gargajiya da kuma na kasashen waje ga ‘yan mata wadanda suka isa aure da kuma matan auren kansu.” Inji Aisha.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel