Abinda ya kamata ku sani game da Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya, Boss Mustapha

Abinda ya kamata ku sani game da Sakataren Gwamnatin Tarayyar Najeriya, Boss Mustapha

Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya mai suna Boss Gida Mustapha lauyane, dansiyasa ga shi kuma gagarumin dan kasuwa.

Mustapha dan asalin Jihar Adamawa ne kuma ya halarci makarantar Hong Secondary School dake karamar hukumar Hong ta Adamawa. Bayan nan yayi karatu a North East College of Arts and Sciences Maiduguri, Borno inda ya samu takardun shaidar WAEC da kuma HSC a shekarar 1976.

KU KARANTA:A sanar damu wurin da aka kai Dadiyata, sakon matasan PDP zuwa ga Buhari

Bayan barin Maiduguri sai ya mika zuwa Jami’ar Ahmadu Bello dake Zaria inda ya yi digirinsa na farko a bangaren karatun shari’a, daga shekarar 1976 zuwa 1979. Haka zalika yayi karatun horar da lauyoyi daga 1980 zuwa 1981.

Boss Mustapha yayi aikin bautar kasa na NYSC shekara daya kamar yadda kowa ke yi bayan kammala karatun jami’a. Ya kuma yin aikin bautar kasan nasa ne a Hedikwatar sojin Najeriya.

Bayan ya kammala bautar kasan na shekara daya, Mustapha ya fara aiki da wani kamfanin kasar Italiya mai suna Sotesa Nigeria Limited inda ya rike mukamin babban darkatn kafin barin kamfanin a shekarar 1983.

Sakataren gwamnatin tarayyar ya rike mukamai da dama da suka danganci aikinsa na lauya. Wasu daga cikin wuraren da yayi aiki na gwamnati ne yayin da sauran kuwa masu zaman kansu ne.

Bugu da kari, wani babban abin burgewa dangane da sakataren shi ne rike mukamin kwamitin gudanarwa na gidauniyar Petroleum Trust Fund daga shekarar 2000 zuwa 2007 inda yayi aiki tukuru.

A yanzu haka dai shi ne Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya ya na da mata da yara kuma mutum ne mai son wasan tenis, tafiye-tafiye, fina-finan tarihi da kuma taimakon al’umma.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel