Kiyaye doka da yin biyayya ga shuwagabanni wajibi ne a Kannywood – Bello BMB

Kiyaye doka da yin biyayya ga shuwagabanni wajibi ne a Kannywood – Bello BMB

Shahararren jarumin nan na Kannywood wanda ya kasance mazaunin garin Jos, Bello Muhammad Bello wanda aka fi sani da BMB yayi tsokaci akan halin da Kannywood ke ciki.

Jarumin ya bayyana cewa dole mambobin masana’antar su zamo masu in doka da kuma gimama na gaba da su.

BMB ya jadadda cewa babu wanda ya fi karfin doka a duniya, kuma ya zama dole abi ka’ida idan dai har bai keta haddin addinin Islama ba.

Yace: "Kiyaye doka da yin biyayya ga shuwagabanni matukar basu keta haddin musulunci ba wajibine a masana'antar film (Kannywood)"

A cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Instagram an jiyo jarumin na cewa: “Bai dace ace an zauna haka ba, masana’antar nan akwai wadanda suka kafa ta, mu kuma muka shigo ciki, muka habbakata, saboda haka ba za mu yi sake ba, da wasu za su zo su lalata ta ba, wannan ai yi ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Daga yau 15 ga watan Agusta na fita daga Kannywood – Adam A. Zango

“Kawai sai kowa ya zo, sai a ce an buga albam, an je an saka wanduna an mammatse jiki, an tattube jiki, an saki duniya gani take cewa yan Kannywood ne, saoda haka dole mu fadi gaskiya. Wanda zai ji haushi ya ji haushi, wanda ba zai ji haushi ba ruwansa.

“Mu dai tsakaninmu da Allah muke fadin gaskiya, ya kamata mu samu doka kuma mu dunga girmama na gaba da mu, mu mutunta doka, babu wanda ya fi karfin doka a duniya, babu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel