Ai ga irinta nan: Wani mutum ya gurfana gaban kotu saboda yada labarin karya

Ai ga irinta nan: Wani mutum ya gurfana gaban kotu saboda yada labarin karya

-Wani matashi ya tsinci kansa gaban kotu sakamakon yada jita-jita da kuma labarin karya wanda ba ayi ba

-Daniel dan shekara 35 a duniya shi ne matashin da hukumar 'yan sanda ta maka kara kotun majistare saboda yada labarin karya

Wani mutum mai suna Daniel dan shekaru 35 ya tsinci kansa a gaban kotu da laifin yada labarai marasa tushe game da makwabcinsa.

Hukumar ‘yan sandan jihar Legas ce ta gurfanar da wannan mutumin a wata kotun majistare dake Ebute Meta a ranar Laraba.

KU KARANTA:Kaduna: El-Rufai zai gina kasuwar zamani (Mall) ta N3.9bn

Sai dai duk da haka Daniel ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa a kai. Sufeta Raphel Doney shi ne jami’in ‘yan sandan da ya shigar da karar inda ya ce a wani lokaci cikin watan Agusta ya aikata laifin.

Jami’in dan sandan ya bada labarin cewa, wanda ake zargin ya je yanata yada zancen cewa makwabcinsa ya biya N150,000 zuwa ga iyayen wata yarinya ‘yar shekara 8 da ya lalata.

Doney ya kara da cewa, wannan batu ya janyo ce-ce kuce a tsakanin al’ummar wannan unguwar tasu da kuma iyalan da lamarin ya shafa.

Har ila yau, wannan laifin ya ci karo da sashe na 168 cikin Kundin dokokin manyan laifuka na jihar Legas, 2015 kamar yadda dan sandan ya fadi.

Alkalin kotun, Agbona Tolu ya yanke kudin belin wanda ake tuhumar kan kudi N100,000. Kana kuma ya dage sauraron karar har zuwa 21 ga watan Agusta domin cigaba da shari’ar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel