Yanzu-yanzu: Gwamna Matawalle ya tsige Sarkin Maru

Yanzu-yanzu: Gwamna Matawalle ya tsige Sarkin Maru

-Gwamna Bello Matawalle ya tsige Sarkin Maru da Hakimin Kanoma daga bisa karagar mulki

-Mataimakin gwamnan jihar Zamfara Barrister Mahdi Aliyu Gusau ne ya fitar da zancen tsige wannan sarkin ranar Juma'a

-Ana zargin sarkin da hakimin na da za hannu cikin al'amuran 'yan bindiga da masu satar shanu da suka jima suna addabar Zamfara

Gwamna Bello Muhammad Matawalle na jihar Zamfara ya tsige Sarkin Maru, Alhaji Abubakar Cika da kuma Hakimin Kanoma, Alhaji Lawal Ahmad.

Rahotanni daga jaridar Daily Trust sun bayyana mana cewa, batun tsige wadannan mutum biyu daga kujerar sarki da hakimi ya samu sanya hannun Mataimakin gwamnan jihar, Barrister Mahdi Aliyu Gusau a ranar Juma’a.

KU KARANTA:Toh fah: Birnin Landan yayi baki kirin sakamakon daukewar wutar lantarki (Hotuna)

Tun watan Yunin da ya gabata ne aka dakatar da sarkin tare da hakimin a bisa zarginsu da ake yi da hannu cikin ayyukan ‘yan bindiga da kuma barayin shanu a jihar Zamfara.

Wannan dalilin ne ya sanya, Matawalle ya kafa kwamitin bincike wanda ya samu jagorancin tsohon Sufeto janar na ‘yan sanda M.D Abubakar.

Bayan kwamitin ya kammala tattara bayanai game da binciken, a karshe wannan kwamiti ya aminta da cewa a cire sarkin da hakimin daga bisa karagar mulki.

Hakimin na Kanoma ya kasance ya na karkashin masautar Maru kamar yadda bayani ya zo mana.

Sanarwa ta musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel