Allah mai iko: Wata mata ta haifa ‘yan biyu bayan ta shekara 11 babu haihuwa (Hoto)

Allah mai iko: Wata mata ta haifa ‘yan biyu bayan ta shekara 11 babu haihuwa (Hoto)

Wata mata mai suna Chinyere Oranwa ta haifi tagwaye bayan ta shekara 11 tare da maigidanta babu haihuwa.

Allah mai iko: Wata mata ta haifa ‘yan biyu bayan ta shekara 11 babu haihuwa (Hoto)
Chinwere Oranwa
Asali: Twitter

KU KARANTA:Dakarun sojin Najeriya sun cikawa Wike aiki na kama Bobrisky

‘Yar uwarta Jennifer Ugwu ce ta watsa hoton mahaifiyar da ‘yan tagwayenta a shafukan sada zumunta, inda ta rubuta cewa: “Godiya ta tabbata ga Allah! ‘Yar uwata Chinyere Oranwa ta haifi ‘yan tagwaye bayan shekara 11 da aurenta, Allah anbin godiya gaskiya ina cike da farin ciki ni kam.”

A wani labarin kuwa zaku je cewa, sojojin Najeriya sun samu nasarar kama dan ta'addan nan mai suna Bobrisky wanda Gwamnan Rivers Nyesom Wike yayi alkawarin duk wanda ya kama shi zai masa kyautar miliyan N30.

Rahotannin da muka samu daga jaridar Daily Trust sun sanar damu cewa a cikin kasa da awa 24 sojojin suka kama Bobrisky na Gokana kamar yadda ake kiransa. Bobrisky rikakken dan daba ne wanda gwamnatin Rivers ta dade tana farautarsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel