Dama ta samu: Hukumar tsaro ta farin kaya tana daukan aiki a yanzu

Dama ta samu: Hukumar tsaro ta farin kaya tana daukan aiki a yanzu

Ma’aikatar cikin gida na Najeriya na sanar da yan Najeriya, musamman matasa cewa ta fara karbar takardun duk masu sha’awar aiki a hukumar tsaro ta farin kaya watau Civil Defence, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Rukunin farko da mutanen da hukumar k enema sun hada da Likitoci, Likitocin hakora, da kuma liktan ido, wadanda take bukatar su nuna shaidar kammala karatun digiri da shaidar lasisin fara aiki daga wajensu.

KU KARANTA: Kalli wani Alhaji yana dawafi dauke da mahaifiyarsa a wuyarsa

Dama ta samu: Hukumar tsaro ta farin kaya tana daukan aiki a yanzu
Civil Defence
Asali: Facebook

Rukuni na biyu kuwa sune jami’ai masu mukamin Inspekta, hukumar tana bukatar mutanen da suka yi karatun jinya da kuma unguwar zoma, inda take neman su kasance suna da rajista da cibiyar unguwar zoma ta Najeriya.

Sai kuma matakin mataimakin Inspekta na I, wanda hukumar ke neman mutanen dake da takardar Difloma a ilimin kiwon lafiyar al’umma, tattara bayanan marasa lafiya, kimiyyar hada magani, abinci da gina jiki, ilimin bayanan kiwon lafiya, ilimin gwaje gwajen kiwin lafiya da sauransu.

Haka zalika hukumar tana bukatar mutanen da suka kware wajen tukim watau direbobi da sauran masu sana’ar hannu. Gaba daya ana bukatar duk masu son shiga wannan aiki su bi ta adireshin yanar gizo kamar haka www.cdfipb.careers inda zasu cike bayanansu tare da sauko da takardun da wadanda zasu tsaya musu zasu cika.

Hukumar ta sanya makonni 4 don neman wadannan guraben aiki, daga ranar 10 ga watan Agusta zuwa 7 ga watan Satumbar 2019. Sai dai hukumar ta nemi duk mai son aikin nan ya kasance dan Najeriya ne, yana da shaidun kammala karatu, yana da cikakken lafiya, ba’a taba daureshi a kurkuku ba.

Haka zalika dole mutum ya kasance baya cikin kungiyoyin matsafa da yan daba, bai taba sata ba, kuma ya kasance shekarunsa basu yi kasa da shekara 18 ko ya haura 30 ba, tsawonsa kada ya yi kasa da mita 1.65 ga maza, da mita 1.60 ga mata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel