Birane 5 mafi kyawon ziyara a duniya

Birane 5 mafi kyawon ziyara a duniya

Kamar dai yadda masu iya magana kan ce, tafiya mabudin ilimi tabbas wannan maganar ta su haka take. Idan har mutum ya kasance ma’aboci tafiye-tafiye ne to kuwa bai taba zama daya da wanda kullum yana kunshe wuri guda.

Ta hanyar tafiye-tafiye mutum kan rage ma kansa damuwa da kuma tunanin abin duniya, musamman a lokutan hutu idan mutum ya samu sariri ba zuwa wurin aiki akwai wuraren da zai iya ziyara domin su debe masa kewa.

Wannan labarin zai kawo maku kyawawan birane biyar da idan har kuka samau ziyarta za ku dawo cike da farin ciki.

KU KARANTA:Yau Buhari zai tafi Daura hutun babbar sallah

Ga jerin sunayen birane 5 mafi kyawon ziyara a duniya:

1. Paris

Ana yi ma wannan birnin lakani da birnin haske, ba wai an sa masa wannan sunan bane babu wani dalili. Birnin Paris birni ne mai matukar kayatarwa saboda akwai wuraren bude ido da dama a cikinsa game da gidajen tarihi. Har ila yau a birnin ne shahararren hatsumiyar nan ta Eiffel Tower take.

2. Rome

Birnin Rome gari ne mai dimbin tarihi, saboda idan ka bibiyi tarihi za ka samu fitattun mutane da dama da suka fito daga garin irinsu Octavian, Julius Caesar, Hadrian da sauransu. Akwai wuraren tarihi da yawan gaske a garin wanda idan kaje sau daya zaka so ka sake komawa.

3. Dubai

Garin dadi na nesa, hutu Dubai abin sha’awa ne saboda gari ne wanda aka kawatasa daidai da zamani. Wani abin mamaki da birnin kullum kara cigaba yake. Birnin Dubai shi ked a gini mafi tsayi a duniya da kuma kanti sayen abubuwa mafi girma a duniya.

4. New York

Birnin New York shi ne mafi shahara daga cikin biranen kasar Amurka. Akwai manyan gine-gine masu tsawo iya kallon mutum a birnin. Wuraren cin abinci kuwa sai wanda ka zaba akwai bila adadin.

5. London

Birnin Landan gari ne mai dimbin tarihi, cike yake da wuraren tarihi da kuma bude ido. A cikin birnin na Landan akwai Tower of London mai dubun tarihi, gidan tarihin British Museum da kuma masarautar Buckingham. Ga wanda bai son sanyi sosai sai ya bari sai tsakankanin watan Maris zuwa Mayu kafin ya ziyarci Landan. Amma ko shakka babu idan kaje sau daya sai ka bukaci sake komawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel