Matawalle ya sallami dukkanin sakatarorin kananan hukumomin Zamfara 14 daga aiki

Matawalle ya sallami dukkanin sakatarorin kananan hukumomin Zamfara 14 daga aiki

-Bello Matawalle ya kori sakatarorin kananan hukumomin Zamfara 14 daga aiki inda ya sauyasu da sabbin mutane

-Gwamna ya sake nada Dr Sha'ayau Mafara a matsayin shugaban kwalejin kimiyya da kere-kere ta Abdu Gusau dake Talata Mafara

-Ibrahim Gusau shi ne sabon shugaban kwalejin ilimi ta Maru wato COE, Maru

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle a ranar Laraba ya sallami dukkanin sakatarorin kananan hukumomi 14 dake Zamfara inda ya nada wasu sabbi.

Haka zalika, Gwamnan ya nada sabbin shugabanin kwalejin kimiyya da kere-kere da kuma kwalejin ilimi ta jihar Zamfara.

KU KARANTA:An hana wata mata zaman majalisa yayin da ta shigo da jaririya rike a hannunta (Hotuna)

Wannan labarin ya fito ne a wani zancen da ya samu sa hannun Daraktan lamuran yada labaran gwamnan, Yusuf Idris a Gusau.

Gwamnan ya umarci dukkanin sakatatorin da aka sallamar da suka mika takardunsu na murabus zuwa ga Ma’aikatar kananan hukumomin jihar.

Sabbin sakatorin kananan hukumomin da gwamnan ya nada sun hada da: Abubakar Bakura (Karamar hukumar Bakura), Rabi’u Pamo ( Anka), Abdulkadir Gora ( Birnin Magaji), Lawali Zugu ( Bukkuyum), Sani Mainasara ( Bungudu), Rabi’u Hussaini (Gummi) da Nura Musa ( Gusau).

Sauran kuwa sun hada da, Bashir Bello (Kaura-Namoda), Ahmadu Mani (Maradun), Salisu Yakubu (Maru), Abba Atiku (Shinkafi), Ibrahim Garba (Talata-Mafara), Aliyu Lawali (Tsafe) da Bala Dauran (Zurmi).

Zancen ya cigaba da cewa, Dr Sha’ayau Mafara shi ne aka bai wa mukamin Shugaban kwalejin kimiyya da kere yayin da Muhammad Maradun kuma ya samu mukamin Rajistara na Kwalejin kimiyya da kere-kere ta Abdu Gusau dake Talata-Mafara.

Bugu da kari, Matawalle ya nada Ibrahim Gusau a matsayin Shugaban Kwalejin Ilimi ta Maru wato COE, Maru.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel