Muna zinace-zinace da shan kwayoyi da sunan jihadi - Tubabben Boko Haram

Muna zinace-zinace da shan kwayoyi da sunan jihadi - Tubabben Boko Haram

- Wani matashi ya bayyana yadda rayuwar sa ta kasance bayan ya shiga kungiyar Boko Haram

- Ya bayyana cewa an yaudare su ne da sunan addini aka yi musu hudubar shedan suka shiga kungiyar

- Ya ce ya san cewa addinin Musulunci ya hana zina, amma kuma su babu abinda suke yi sai zina da shaye-shaye

Wani dan kungiyar Boko Haram da ya tuba ya bayyana yadda shugabannin kungiyar suka yaudare shi da sunan jihadi aka suka jefa shi cikin bala'i da masifa.

Idan ba a manta ba kungiyar dai ta jawo hankalin matasa da yawa a kasar nan, inda suka dinga rububin shiga cikinta, yayin da kuma wasu wanda basu da ra'ayin shiga ta tilasta su ta dole bayan ta sace su, sannan ta dinga yi musu barazanar kisa idan har suka sake suka fita daga cikinta.

Wani matashi tsohon dan kungiyar wanda ya tuba yanzu ya bayyana cewa rashin aikin yine ya jefa shi cikin wannan harkar.

"Sun yaudare mu ne ta hanyar yi mana da'awa da addinin Musulunci, sai da muka duba muka gani cewa ashe ba Musulunci ba ne," a cewar matashin da ya tuba daga harkar kamar yadda ya bayyanawa jaridar BBC.

Saurayin ya bayyana cewa a lokacin kafin su shiga kungiyar, suna ganin wani abokinsu yana zuwa da kudi, yayin da su kuma suke ta kokarin ganin yadda zasu yi su samu kudin sun asa.

Ya cigaba da cewa abokin nasu ya ja wasu daga cikinsu, inda da farko ake biyansu naira dubu uku a duk lokacin da suka kai hari, ko kuma suka kwato kudi ko kuma aka biyasu kudin fansa.

KU KARANTA: Tirkashi: Budurwa tayi ta surfawa saurayinta zagi kala-kala bayan ta gano cewa yana zuwa yayi lalata da kawarta

Ya ce a lokacin abin da ake ba su bai wuce Naira 3,000 ba, kuma za a ce akwai manya wadanda za su zo su ba su Naira dubu 500 ko dubu 600.

Matashin wanda ya shafe shekara takwas tare da Boko Haram, ya ce da farko yana jin dadin cewa addinin Musulunci yake yi wa aiki. Amma daga baya da ya gano cewa kungiyar ta kauce wa addinin Musulunci ya shiga damuwa sosai.

“Ga Kur’ani a ajiye, na duba na ga Allah Ya hana zina, ya hana shaye-shaye, sai na ga cewa ga kwayoyin, ga zinar, a kamo mata a zo a yi ta zina da su, wani ma bai damu da Sallah ba kuma za a zo a kashe wanda yake Sallar,” inji shi.

Daga karshe matashin tare da wadansu takwarorinsa 20 sun yanke shawarar barin kungiyar, bayan da suka gaji da kuncin rayuwa da suke fuskanta. Sannan suka mika kansu ga sojojin Najeriya, inda daga baya aka koyar da su sana’o’i.

A yanzu matashin ya koyi sana’ar kafinta, kuma ya ce rayuwarsa ta inganta, domin yana yin aiki ana biyansa, kuma yana samun karbuwa a sana’ar ta sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel