Duniya ina za ki damu: ‘Yan sanda sun kama gurgu dan shekara 69 wanda ke kerawa ‘yan fashi bindiga a Enugu

Duniya ina za ki damu: ‘Yan sanda sun kama gurgu dan shekara 69 wanda ke kerawa ‘yan fashi bindiga a Enugu

-Yan sandan Enugu sun kama wani hatsabibin tsoho wanda ke samar da bindigogi ga 'yan fashi a jihar

-Cyprian Eze wanda yake gurgu kuma dan shekara 69 ya kasance shi ne ke bai wa yan fashi da yan kungiyar asiri bindigogi kamar yadda kakakin yan sandan jihar ya fadi

-A ranar Litinin 5 ga watan Agusta jami'an yan sandan Enugu suka samu cafke tsohon

An kama wani hatsabibin tsohon mai shekaru 69 a duniya wanda ke sarrafa bindigogi yana bai wa ‘yan fashi a Jihar Enugu.

Majiyar Daily Trust ta sanar damu cewa, tsohon mai suna Cyprian Eze wanda yake gurgu, yana zaune ne a Umuabi dake karamar hukumar Idi ta jihar Enugu. Ya dade yana bai wa yan ta’adda bindigogi domin sun gudanar da harkokinsu.

KU KARANTA:Bamu da labarin sakin El-Zakzaky – IMN

Wata majiyar ta sanar damu cewa, a ranar Litinin 5 ga watan Agusta ne jami’an ‘yan sanda suka mamaye mabuyar Cyprian da sanyin safiya, kana suka samu tasa keyarsa gaba.

A wani zance da Kakakin yan sandan jihar, SP Ebere Amaraizu ya fitar ya ce: “ Wannan mutumin ya dade yana kera bindigogi yana bai wa ‘yan fashi da kuma ‘yan kungiyar asiri.

Amaraizu ya cigaba da cewa: “ Ya fada mana yadda yake kera bindigogin nasa da kuma yadda yake sada su zuwa ga abokan harkarsa wadanda ‘yan fashi ne mafi yawancinsu da kuma ‘yan kungiyar asiri.”

Kakakin ‘yan sandan ya kara da cewa, “ Yanzu haka mutumin na hannunmu kuma zai taimaka mana wajen cigaba da binciken kamo sauran abokan sana’ar tasa.”

An samu bindigogi kala-kala tare da Eze, a ciki hadda wata fisto mallakar shugaban wata kungiyar asiri mai suna Black Axe wadda ya kawo domin a gyara masa ita.

Har ila yau, akwai wasu bindigogin iri daban-daban da kuma damin harsashi da aka samu tare da mutumin a lokacin da aka kama shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel