Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 5 a Yola

Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 5 a Yola

-Ambaliyar ruwa ta kashe mutum biyar a Yola babban birnin Adamawa

-Sakataren hukumar bayar da agajin gaggawa na jihar Adamawa Dr Mohammed Sulaiman ne ya tabbatar da aukuwar lamarin ga manema labarai

-Mutum biyar din da suka rasu dukkaninsu yara ne guda hudu da kuma jariri daya a cikinsu

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa wato ADSEMA ta tabbatar da mutuwar mutum biyar a ciki hadda jariri sakamakon wata ambaliyar ruwa da ta auku a Yola babban birnin jihar.

Dakta Mohammed Sulaiman, Sakataren hukumar ne ya shaidawa manema labarai aukuwar wannan al’amari ranar Juma’a a garin Yola. Sulaiman ya ce lamarin dai ya auku ne da yammancin Alhamis a sakamakon wani ruwa da akayi mai karfi kamar da bakin kwarya.

KU KARANTA:Jiragen sojoji sun yiwa ‘yan Boko Haram barin wuta a Jejin Sambisa

Sulaiman ya ce: “ Ambaliyar ta lalata kayayyaki da dama wadanda adadin kudinsu ya kai miliyoyi. Baya ga asarar kayayyakin amfani kuma, akwai mutum biyar da suka mutu a sanadiyar ambaliyar.”

Ya kara da cewa: “ Wadanda suka rasa rayukansu a dalilin ambaliyar yara ne gudu hudu sai jariri guda daya a cikinsu. Shiyyoyin da abin ya shafa sun hada da; Yolde-Pate, Damare, Wuro-Jabbe, Damilu da Jambutu dake kananan hukumomin Yola ta Kudu da ta Arewa.”

Hukumar bayar da agajin gaggawan ta ziyarci wurin da wannan ambaliya ta auku inda ta kai kayan agaji kamar yadda ta saba.

Daya daga cikin mazauna yankin da ambaliyar ta auku mai suna Malam Kabiru Bello, ya shaidawa manema labarai cewa ya rasa diyansa biyu a sakamakon ambaliyar.

A wani labarin kuwa zaku ji cewa, rundunar sojojin saman Najeriya wato NAF ta ragargaza wata mabuyar mayakan boko haram dake a cikin jejin Sambisa.

A ranar Alhamis dakarun sojin suka yi amfani da jirage biyu domin kai hari mabuyar mayakan dake Alafa cikin Jejin Sambisa. Dakarun sojin sun yi nasarar kashe mayakan tare da tayar da mabuyar gaba dayanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel