Daga karshe, Magajin garin Daura ya koma gida (Hotuna)

Daga karshe, Magajin garin Daura ya koma gida (Hotuna)

Sai a yau, Laraba, 31 ga watan Yuli magajin garin Daura, Alhaji Musa Uba ya samu damar komawa mahaifarsa ta Daura bayan kwashe kimanin wata guda daya cur yana hutawa tare da duba lafiyarsa a babban birnin tarayya Abuja.

Legit.ng ta ruwaito Magajin gari ya samu kyakkyawar tarba daga masoya, yan uwa da abokan arziki, kai har ma da mai martaba Sarkin Daura kansa, Alhaji Faruk Umar, tare da yan fadarsa inda suka yi maraba dashi hannu biyu biyu.

KU KARANTA: Rikicin kabilanci a yayi sanadiyyar kulle wata jami’a a jahar Taraba

Daga karshe, Magajin garin Daura ya koma gida (Hotuna)
Daga karshe, Magajin garin Daura ya koma gida (Hotuna)
Asali: Facebook

Idan za’a tuna a ranar 1 ga watan Mayun shekarar 2019 ne wasu gungun yan bindiga suka yi awon gaba da Magaji a kofar gidansa bayan sallar magariba yayin da yake zaune tare da jama’a yana jiran lokacin sallar Isha’I kamar yadda ya saba a kullum.

Sai bayan watanni biyu cur a hannun miyagun masu garkuwa sa’annan jami’an tsaron Najeriya a karkashin jagorancin mataimakin kwamishinan Yansandan Abba Kyari suka kubutar dashi daga mabuyar barayin dake cikin garin Kano.

Daga wannan rana ne aka kai Magaji gidansa dake Daura domin ganawa da iyalansa, daga bisani kuma aka wuce dashi babban birnin tarayya Abuja, sai kuma yau ya koma gida.

Daga karshe, Magajin garin Daura ya koma gida (Hotuna)
Magaji
Asali: Facebook

Daga karshe, Magajin garin Daura ya koma gida (Hotuna)
Magaji
Asali: Facebook

Daga karshe, Magajin garin Daura ya koma gida (Hotuna)
Magaji
Asali: Facebook

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel