Sallah: Kada ku ci bashi don siyan ragon layya – Malamai sun yi gargadi

Sallah: Kada ku ci bashi don siyan ragon layya – Malamai sun yi gargadi

Malaman addinin Musulunci a Omu-Aran, jihar Kwara, a ranar Laraba, 31 ga watan Yuli sun gargadi Musulmai da su guje na cin bashi mara amfani domin siyan ragon layya.

Malaman, wadanda suka yi gargadin a zantawa daban-daban da suka yi da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) Omu-Aran, sunce yanka ragon layya, kamar aikin hajji, wajibi ne ga wadanda ke da karfi night aljihu.

Malaman sun lura cewa wannan lamari kan haifar da rikici a tsakanin mutane bayan sallah.

Alhaji Sodiq Afolayan, babban limamin masallacin Juma’a na Omu-Aran yace, musulunci bata yadda da almubazaranci ba kamar yadda addinin ya haramta hakan.

Har ila yau Alhaji Mustapha Abdulsalam, wani malamin addini, ya bukaci Musulmai da su gaji siyan raguna marasa lafiya don yin layya.

KU KARANTA KUMA: Na fi jin dadin yin lalata da kananan yara maza, in ji wani gardin dan luwadi da aka kama

Ya kuma jadadda cewa siyan ragon layya ba wajibi bane, maimakon haka ya bukaci iyaye da su mayar da hankali wajen biyan kudin makarantan yaransu da wasu muhimman abubuwa da ake bukata na yau da kullun, maimakon matsawa da takura kai wajen yin abunda mutum bai da karfin yi.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel