Gwamnatin kasar Kenya ta kori Yesu, ta kama faston da ya gayyato shi

Gwamnatin kasar Kenya ta kori Yesu, ta kama faston da ya gayyato shi

- Faifan bidiyon bullar wani bature da ya yi ikirarin cewa shine 'Yesu Almasihu' sun mamaye dandalin sada zumunta da kafafef yada labarai a kasar Kenya

- An gano cewa wasu limaman Coci ne suka gayyato baturen tare da shaida wa mabiyansu shine 'Yesu Almasihu' da ake cewa zai dawo a karshen duniya

- Yanzu haka gwamnatin kasar Kenya ta kori Yesun na bogi tare da kama mayaudaran Fastocin da suka gayyato shi kasar

Gwamnatin kasar Kenya ta kori wani bature da ke gabatar da kansa a matsayin 'Yesu Almasihu' tare da kama wasu limaman Coci da suka gayyato shi tare da shaida wa mabiyansu cewa shin dan Allah na gaske.

Wasu limaman Coci su biyu ne suka gayyato baturen zuwa kasar tare da gamsar da mabiyansu cewa shine Yesu Almasihu da aka yi alkawarin cewa zai dawoa karshen duniya.

Baturen, da ke gabatar da kansa a matsayin Yesu Almasihu, ya na yawo a cikin kasar Kenya tare da karbar kudi daga hannun jama'a domin nuna musu mu'ijiza da kuma yi musu tanadin wurin zama a gidan Aljanna idan sun mutu.

DUBA WANNAN: Da zafinsa: Kotu ta kwace kujerar PDP a majalisar wakilai, ta bawa APC

Hankalin mahukuntan kasar Kenya ya kai kan mutumin ne bayan faifan bidiyonsa ya mamaye dandalin sada zumunta da kafafen yada labarai na kasar da ketare.

Jaridar Daily Afrika ta rawaito cewa yanzu haka gwamnatin kasar Kenya ta kori Yesun na bogi tare da kama mayaudaran Fastocin da suka gayyato shi kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel