Rundunar Sojin Najeriya ta bude sabuwar bataliya a maihafar Buhari

Rundunar Sojin Najeriya ta bude sabuwar bataliya a maihafar Buhari

-Rundunar Sojin Najeriya ta bude sabuwar bataliya a Daura

-Sabuwar bataliyar mai suna 171 Battalion za ta samu Laftanal Kanal ne a matsayin jagoranta kuma 17 Infantry Brigade dake Katsina ce za ta rika ba ta oda

-An bude wannan bataliyar ne domin fada da ta'addanci a arewacin Jihar Katsina yankin da ke kusa da Jamhuriyar Nijar

A cikin watan nan rundunar Sojin Najeriya ta bude wata katafariyar bataliya a mahaifar Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta Daura dake Jihar Katsina.

Bataliyar mai suna 171 Battalion an bude ta ne domin fada da ta’addanci da kuma muggan laifuka a yankin arewacin jihar Katsina wanda ke daf da kan iyakar jamhuriyar Nijar. Majiyar sojin ce ta ba jaridar Premium Times wannan labarin.

KU KARANTA:Cin-hanci da rasahwa ne ke haifar mana da matsalolin tsaro, inji Magu

Har wa yau, majiyar ta sake cewa bataliyar za ta taimakawa ayyukan 17 Infantry Brigade da kuma 35 Battalion dake babban birnin jihar ta Katsina.

Sabuwar bataliyar wadda za ta kasance karkashin jagorancin Laftanal Kanal daban ce da ta Fort Muhammadu Buhari wadda aka kaddamar a Dauran a watan Mayun 2017 wadda kuma har ila yau ke karkashin umarnin 35 Battalion.

Dukkanin bataliyoyin biyu da 35 Battalion ta Katsina da 171 Battalion ta Daura zasu rika karbar oda ne daga 17 Infantry Brigade dake Katsina.

Tun shekarar 2015 da Buhari ya zamo shugaban Najeriya, tsaro a jiharsa ta haihuwa da wasu jihohin dake makwabtaka da ita sake lalacewa yake yi har yanzu.

An riga da an bude 171 Battalion a Daura kuma an umarci dukkanin wata cibiyar sojin kasar nan da ta kawo jami’ai inda ake bukatar mutum 350 domin fara aiki a wannan bataliya.

Bude wannan bataliyar ya biyo bayan wasu guda biyu ne da rundunar sojin ta bude a jihohin Sokoto da Rivers domin sake karfafa tsaro a yankunan Arewa maso yamma da kuma Kudu maso kudancin Najeriya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel