Cin-hanci da rasahwa ne ke haifar mana da matsalolin tsaro, inji Magu

Cin-hanci da rasahwa ne ke haifar mana da matsalolin tsaro, inji Magu

-Ibrahim Magu ya fadi abinda ke haddasa karuwar rashin tsaro a kasar nan

-Shugaban hukumar ta EFCC ya ce cin-hanci da rashawa ne musabbabin aukuwar matsalolin tsaron Najeriya a hira da wani gidan rediyon Ibadan

-Magu ya samu wakilicin shugaban hukumar EFCC na Ibadan a lokacin shirin da aka yi ranara Talata

Mukaddashin Shugaban Hukumar yaki da cin-hanci da kuma yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC, Ibrahim Magu ya daura laifin tabarbarewar tsaron kasar nan kan cin-hanci da rashawa.

Magu yayi wannan bayanin ne a wata hira da ya yi da gidan rediyon Ibadan mai suna Diamond 101.1 FM a cikin shirinsu mai suna Eagle Alert ranar Talata.

KU KARANTA:Shi’a: Haramta IMN tamkar take musu hakkin yin addini ne, inji HRW

Magu wanda Shugaban hukumar EFCC na Ibadan, Friday Ebelo ya wakilta a lokacin da ake shirin ya ce, cin-hanci da rashawa ya bude kofar aikata muggan laifuka bila-adadin a kasar nan.

Ebelo ya ce: “ Ba zaka iya bambance lalacewar tsaro da cin-hanci da rashawa ba a kasar nan. Hanya daya tilo wadda zamu bi domin ceto kasar mu daga cikin wannan hali ita ce mu kawar da rashawa, sai kasarmu ta zauna lafiya.

“ Idan mu kayi nasarar dakile cin-hanci a kasar nan, zamu samu abubuwa da dama cikin sauki ta yadda za a samu yin manya-manyan ayyukan gina kasa cikin sauki, tare da samar da aikin yi ga marasa aiki musamman matasa a kasar nan.

“ Dole sai iyayen yara sun bada hadin kai wurin tarbiyar diyansu, ta hanyar tura yaran nasu makaranta domin neman ilimi, wannan ma abu ne wanda zai matukar taimakawa wannan kuduri.” A cewar Ebelo.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel