Real Madrid ta fada wa James zai cigaba da zama a kulob din

Real Madrid ta fada wa James zai cigaba da zama a kulob din

-Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta fadawa dan wasan Columbia James cewa zai cigaba da zamansa a kulob din

-Majiyar ESPN ce ta kawo mana wannan labarin inda ta ce raunin da Asensio ya samu ne ya sanya Madrid ta canza shawarar sayar da dan wasan

-Kafin Madrid ta yanke wannan hukuncin akwai kungiyoyin nahiyar turai da dama da suka nuna sha'awar samun dan wasan

Real Madrid ta fadawa James Rodriguez cewa zai iya tsayawa a kulob din cikin kakar wasa mai zuwa wadda ake shirin farawa nan da kwanaki kadan, majiyar ESPN FC ce ta sanar damu wannan labarin.

James dan asalin kasar Columbia, ya dawo kulob dinsa na Real Madrid bayan ya kwashe kakar wasa biyu a mazaunin dan aro a kasar Jamus inda ya takawa kulob din Bayern Munich leda. A shekarar 2014 Real Madrid ta saye shi kan kudi miliyan €80.

KU KARANTA:Da zafinsa: Kotun Koli ta tsige dan majalisar APC

An dade ana tunanin dan wasan zai sauya sheka musamman bisa la’akari da alaqa da tayi tsami tsakaninsa da kocin Real Madrid wato Zinedine Zidane.

Kungiyoyin kwallon kafa da dama su na zaurancin dan wasan, a cikin hadda Atletico Madrid wadda take abokiyar adawa ga Real Madrid mafi kusa saboda suna zaune a gari guda. Bayan Atletico kuma akwai Napoli, kulob din da tsohon kocin Madrid ke jagoranta a yanzu wato Carlo Ancelotti.

Bayan dawowar James daga hutunsa kasancewar ya fafata a gasar cin kofin Nahiyar Amurka wanda aka fi sani da Copa America, sai kulob dinsa na Madrid ke nuna masa yana cikin lissafinta na kakar wasan bana.

Har ila yau, wata majiyar ta sanar damu cewa, abubuwa kan iya canzawa amma dai a halin yanzu, shugabannin kulob din Madrid na kallon James a matsayin dan wasan dake cikin lissafin kulob din, musamman bayan da Marco Asensio ya samu wani mummunan rauni a mako da ya gabata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel