Hotuna: Cikin hawaye, an gudanar da jana’izar matashin da rikicin ‘yan shi’a ya rutsa da shi

Hotuna: Cikin hawaye, an gudanar da jana’izar matashin da rikicin ‘yan shi’a ya rutsa da shi

-An yi jana'izar Precious Owolabi da safiyar Alhamis a Zariya

-Precious Owolabi shi ne matashin nan da ya rasu yana bakin aiki sakamakon rikicin yan sanda da 'yan shi'a a Abuja

-Buhari zai tafi kasar Liberia da safiyar Juma'a inda ake sa ran dawowarsa da yammacin ranar ta Juma'a

A safiyar ranar Alhamis ne aka gudanar da jana’izar marigayi Precious Owolabi wanda ke dauko ma gidan talabijin na Channels TV rahoto a makabartar Wusasa dake Zariya.

Hotuna: Cikin hawaye, an gudanar da jana’izar matashin da rikicin ‘yan shi’a ya rutsa da shi
Jana'izar Precious Owolabi
Asali: Twitter

KU KARANTA:El-Zakzaky: Gwamnatin Buhari na tattaunawa da ‘yan Shi’a

Wannan matashin dai ya gamu ne da ajalinsa ne a yayin da yake kokarin daukar rahotanni game da zanga-zangar ‘yan shi’a wadda ta rikide zuwa rikici ranar Litinin a Abuja, . Kafin rasuwarsa, matashin ya kasance yana aiki tare da gidan talbijin na Channels TV a matsayin dan bautar kasa.

Hotuna: Cikin hawaye, an gudanar da jana’izar matashin da rikicin ‘yan shi’a ya rutsa da shi
Gawar Precious
Asali: Twitter

Hotuna: Cikin hawaye, an gudanar da jana’izar matashin da rikicin ‘yan shi’a ya rutsa da shi
Owolabi Precious

A wani labarin kuwa, zaku ji cewa Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari zai bar Abuja ranar Juma’a zuwa kasar Liberia inda zai halarci taron bikin samun ‘yancin kasar karo na 172.

Shugaba Muhammadu Buhari shi ne zai kasance babban bako na musamman wurin taron. Bugu da kari, zai karbi wata babbar lambar girma mai taken “ The Grand Cordon of Knighthood of Venerable Order of the Pioneers” wadda ita ce lambar girma ta farko a kasar Liberia.

Gwamnatin Liberia ke bada wannan lamba ta girma a bisa fice a bangaren lamuran da suka shafi kasa da kasa, gwamnatoci, addini, kimiyya ko cinikayya da dai sauransu.

Gwamnonin jihohin Najeriya uku ne zasu raka Shugaba Buhari kasar ta Liberia, wadannan gwamnonin kuwa sun hada da; Kayode Fayemi na Ekiti, Abdulrahman Abdulrazaq na Kwara da Mai Mala Bunin a jahar Yobe. Ana tsammanin dawowar Shugaban da yammacin Juma’a.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel