Wani mutum ya gurfana gaban kotu da laifin damfarar N2.7m

Wani mutum ya gurfana gaban kotu da laifin damfarar N2.7m

-Wani matashi ya damfari abokin aikinsa kudi naira miliyan 2.7

-Matashin da hukumar 'yan sandan Legas ta maka kara kotu ya qi amsa laifin da ake tuhumarsa da aikatawa

-Alkalin kotun ta dage sauraron karar har zuwa 12 ga watan Agusta, 2019

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas a ranar Laraba ta shigar da karar wani dillalin matafiya, Oluwasegun Gbeleye a kotun Majistare dake Surulere, inda ake zarginsa da damfarar N2.7m kudin yin bizar Australia.

Gbeleye wanda aka boye mazauninsa, ya bayyana gaban kotun ne inda ake tuhumarsa da aikata laifuka dai-dai har guda hudu, laifukan sun hada da; damfara, zamba cikin aminci, karya da kuma sata.

KU KARANTA:Babbar magana: Mataimakin gwamnan Kogi zai kai karar gwamnansa kotu

Sai dai kuma wanda ake tuhumar ya qi amsa ko daya daga cikin laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa.

Alkalin kotun, Misis Oluyemisi Adelaja ta bada belinsa kan kudi N500, 000. Daga bisani mai shari’ar ta dage karar har zuwa ranar 12 ga watan Agusta, 2019.

Gabanin jin ta bakin Alkalin kotun, jami’ar yan sandan da ta shigar da karar, Sajan Anthonia Osayande ta shaida ma kotun cewa, " Mutumin da take karar ya damfari wani Prince Nnadozie ne a cikin watan Maris na 2018 a asibitin Randle General Hospital.

Osayande yayi amfani da dubara inda ya karbi N2.7m daga hannun Nnadozie kan cewar zai nema masa bizar shiga Australia har guda biyar da kuma lasisin yin aiki a kasar, amma sai dai ya gagara samar da ababen da ya ambata."

Anthonia ta cigaba da cewa: “ Wannan mutumin ya bugo biza ta bogi guda biyar ya bai wa Prince kana shi kuma yayi hidimar gabansa da kudin da ya bashi.”

Ko da Nnadozie ya farga cewa wannan mutumin cutarsa kawai zaiyi, sai ya nemi ya dawo masa da kudinsa amma ya qi inda yake cewa yana kan yin aikin ne har yanzu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel