Israila ta rushe gidajen Falastinawa da ya raba kasashen biyu

Israila ta rushe gidajen Falastinawa da ya raba kasashen biyu

-Dubban dakarun sojin isra’ila da motocin rushe-rushe suka rushe gidajen Falastinawa kusa da Sur Baher duk da zanga-zanga da kushe daga kasashen duniya.

-Mazauna kauyen Wadi al-Hummus suka shaida wa manema labarai, ranar litinin cewa gine-gine 16 masu kimanin muhallai 100 aka rushe.

Dubban dakarun sojin isra’ila da motocin rushe-rushe suka rushe gidajen Falastinawa kusa da Sur Baher duk da zanga-zanga da kushe daga kasashen duniya.

Mazauna kauyen Wadi al-Hummus suka shaida wa manema labarai, ranar litinin cewa gine-gine 16 masu kimanin muhallai 100 aka rushe.

“ An fara shiryen-shiryen da tsakiyar dare inda dakarun sojojin Israila dauke da makamai ke rakiyar motocin rushe gine ginen suka shigo garin". An yi barazana ga iyalan dake cikin gine-ginen inda aka tashe barci sa’annan aka kore su daga cikin gidajen,” cewar kungiyar neman yancin falastinawa (PLO).

Dakarun sojin israila dai na ganin gidajen wanda sun yi kusa da bangon daya raba Falastinu da wurin da Israila ta mamaye a matsayin barazana.

Babbar Kotun kasar Israila ta yanke hukuncin rushe gidajen a watan jiya, wanda hakan ya kawo karshen doguwar shari’ar bayan shekaru bakwai, kuma ta bada ranar litinin don su fice daga gidajen nasu. Falastinawa dai na ganin hakan somin tabi ne ga sauran garu-ruwan dake kusa da katangar wanda suke da nisan dubban kilomita da wannan marraba.

KARANTA WANNAN: Karin albashi: Neman abin da ba zai yiwu ya ke kawo cikas – Oyo - Ita

Kauyen Sur Baher na dai kusa da bangon da ya raba gabashin Jerusalam da wurin da Israilawa suka mamaye a yakin shekarar 1967.

Wakilin mu yace sun jiyo ihu da kara daga iyalai, sai dai bayan awa biyu kasha 50 cikin gidajen an rushes u.

Ministan tsaro na Israila yace mazaunan gurin na daukar doka da hannun su akan gine ginen da sukayi, yace “akwai gine ginen da ba bisa doka aka yi su ba”

Sai dai falastinawa mazauna gurin sun ce suna kar-kashin ikon Falastinu ne kamar yadda sulhun Oslo yace na shekarar 1993.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel