Allahu Akbar: Kasar Saudiyya ta shirya gasar kiran sallah da karatun Al’kur’ani
-Kasar Saudiyya ta zata shirya gasar karatun Al-kur'ani da kiran sallah
-Jakadan kasar Saudiyya a Najeriya Adnan Bostaji ne ya sanar da wannan labari ga manema labarai
-Kimanin mutum 21,000 sun riga sun cika takardar neman shiga wannan takarar da zata gudana daga 24 ga Agusta zuwa 24 ga Satumbar wannan shekara
Wata hukuma ta musamman dake karkashin Masarautar Saudiyya na sanar da al’ummar musulmin dake fadin duniya cewa ana cigaba da cika gurbin neman kasancewa cikin gasar karatun Kur’ani da kiran sallah.
A wani zancen da ya fito daga hukumar wanda muka samu a hannun Jakadan kasar Saudiyya a Najeriya, Adnan Bostaji ya ce, an shirya wannan gasar ne domin nunawa duniya al’adun muslunci ta hanyar karatun Kur’ani da kuma kiran sallah.
KU KARANTA:‘Yan sanda sun kashe matasan ‘yan fashi 4 a Edo
A cewar zancen, wannan ya kasance daya daga cikin kudurin kasar Saudiyya na habbaka hukumomi masu zaman kansu a kasar.
An tanadi kyautar kudi Riyal miliyan 5 ($1.3m) ga wanda lashe gasar karatun Kur’ani yayinda wanda yayi nasara a fagen kiran sallah kuwa zai tashi da Riyal miliyan 2 ( $530,000).
Kawowa yanzu, mutane 21,000 ne daga kasashe 162 suka cika takardar neman shiga gasar, inda mutum 11,000 suka cika gasar karatun Kur’ani sai kuma 10,000 da suka cika gasar kiran sallah.
Za’a iya ziyartar wannan shafin na yanar gizo domin cika takardar neman shiga gasar, https://quranathanawards.com
Za kuma a rufe shafin rajistar a karshen watan Yuli. Kuma gasar zata fara daga ranar 24 ga watan Agusta zuwa 24 ga watan Satumba. Fadin suna tare da karrama wadanda sukayi nasara zai soma tun daga ranar 25 ga watan Satumba har zuwa 25 ga watan Oktoba.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng