Fadan Amurika da Iran: Amurika zata ajiye sojojinta a kasar Saudi Arabia

Fadan Amurika da Iran: Amurika zata ajiye sojojinta a kasar Saudi Arabia

-Kasar Amurika zata tura sojojinta da kuma kayan yaki zuwa Saudi Arabia karo na farko tun shekara ta 2003, inji ofishin Pentagon.

-Rundunar ta kai yawan sojoji 500 da kuma makami mai linzami da kuma jirgin yaki kirar F-22.

-Ofishin Pentagon ya bayyana cewa za su kai sojin don kare dakarunta da kuma muradunta a yankin.

Kasar Amurika zata tura sojojinta da kuma kayan yaki zuwa Saudi Arabia karo na farko tun shekara ta 2003, inji ofishin Pentagon.

“Zamu tura dakarun ne don mu kara jan kunne, don kuma mu ta kare dakarunmu da kuma muradunmu a yankin daga barazana” cewar babban ofishin sojin kasar.

Tun bayan ficewar Washington daga yarjejeniyar nukiliya a 2015 fargabar barkewar fada tsakanin Amurika da Iran ke karuwa. Farkon makon nan ne shugaba Donald trump yace Amurka ta halbo wani jigin marar matuki na kasar Iran, wanda Tehran ta karyata.

KARANTA WANNAN: An hallaka wani saurayi saboda budurwa a Jihar Anambra

kafofin yada labarai na Saudiyya sun bayyana cewa Sarkin Saudiyya, Salman: “Ya amince da karbar dakarun sojin domin hadin gwiwa da kuma samar da tsaro mai dorewa a yankin” . Iran ba tada abokiyar tsama kamar kasar Saudi Arabiya.

BBC ta ruwaito cewa rundunar ta kai yawan sojoji 500 da kuma makami mai linzami da kuma jirgin yaki kirar F-22. Dakarun sojin kasar Amurkar dai sun fice daga kasar Saudia Arabia a shekara ta 2003 bayan shekaru goma sha biyu lokacin da kasar Iraq ta mamaye kasar Kuwait a shekarar 1991.

Kwanakin baya Legit.ng ta ruwaito cewa kasar Iran ta halbo wani jirgi marar matuki na kasar Amurka a cikin samaniyar kasar ta Iran. Iran tayi ikirari cewa jirgin na leken asiri ne. Bayan afkuwar hakan ne, shugaba Donald Trump na Amurika ya kara kakaba ma kasar iran takunkumi.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel