An gano wani tsohon masallaci da aka gina tun cikin karni na bakwai a kasar Isira'ila

An gano wani tsohon masallaci da aka gina tun cikin karni na bakwai a kasar Isira'ila

-An gano ragowar wani masallaci wanda ya na daya daga cikin masallatai mafi dadewa a duniya

-Hukumar tarihi ta kasar Isira’ila ta bayyana cewa masallanci wanda aka gano an gina shi ne tun cikin karni na bakwai zuwa karni na takwas

Masu binciken tarhin dan adam ta hanyar hako kasa sun gano ragowar wani masallaci wanda ya na daya daga cikin masallatai mafi dadewa a duniya da aka gina shi tun lokacin da musulunci ya isa kasar Isira’ila daga kasa mai tsarki.

Hukumar tarihi ta kasar Isira’ila ta bayyana cewa masallanci wanda aka gano a wani kauye a garin Rahat a yankin saharar Negev, an gina shi ne tun cikin karni na bakwai zuwa karni na takwas.

Akwai manyan masallatai da aka sani da suka dade kamar wannan wadanda aka gina tun lokacin da musulunci ya isa Jerusalam, amma yana da wahala a samu masallaci mai tarihi irin wannan a kauye da masallatanshi duk manoma ne. Hukumar ta bayyana.

KARANTA WANNAN: Shari’ar Atiku da Buhari: An sha mamaki yayin da shaidan Atiku ya fashe da kuka a kotu

Masallacin wanda aka gano ragowarshi, budadde ne marar rufi da girmanshi bai wuce garejin mota guda daya ba da tabarmar salla dake kallan alkibila.

Hukumar ta bayyana cewa : “Wannan na daya daga cikin masallantan farko da aka gina tun lokacin da musulunci ya iso kasar Isira’ila bayan galabar da Larabawa suka samu na shekarar 636 bayan zuwan annabi Isa.”

Giddeon Givani na hukumar ya ce : “Wannan masallaci da aka gano da garin da aka ganoshi na da matukar mahimmanci ga karatun tarihi a kasar nan musamman a wannan lokacin da ake cike da rudani.”

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel