Kotu ta daure wani mai gadi da ya saci sarkar N10m

Kotu ta daure wani mai gadi da ya saci sarkar N10m

-Kotun majistire a jihar Legas ta daure wani mai gadi , Amos Dauda a gidan yari bayan da ta kama shi da laifin satar sarka da kudinta ya kai Naira miliyan 10

-Dan sanda mai gabatar da kara ya ce an baiwa wanda ake kara amanar makullan gidan don ya share dakin da aka ajiye sarkar

-Mai shari’ah M. O Ope-Agbe ta daure Dauda bayan da ya amsa cewa ya aikata laifin kamar yadda ake tuhumarshi, sa’annan bai nuna alamun yayi nadama ba

A jiya Alhamis, 18 ga watan Yuli 2019, wata kotun majistire dake a Igbosere a jihar Legas ta daure wani mai gadi , Amos Dauda a gidan yari na tsawon shekara uku bayan da ta kama shi da laifin satar sarka da kudinta ya kai Naira miliyan 10.

Mai shari’ah M. O Ope-Agbe ta daure Dauda bayan da ya amsa cewa ya aikata laifin kamar yadda ake tuhumarshi, sa’annan bai nuna alamun yayi nadama ba.

Mai shari’ah Ope-Agbe ta ce: “An daure wanda ake kara shekara uku a gidan yari. Lokacin daurin zai fara tun ranar 24 ga watan Nuwamba na shekarar 2018 a lokacin da aka kamashi. Babu zabin tara.”

KARANTA WANNAN: Babbar magana: Sai da aka yi mini tayin N360m a kowanne wata idan na shiga kungiyar asiri ta 'Illuminati' - Dr Tumi

Dan sanda mai gabatar da kara, sajan Cyriacus Osuji ya bayyana cewa Dauda ya aikata laifin ne da misalin karfe 7:00 na safe a cikin watan Afirilu 2018 a gida mai namba 5 layin Shotidaya, Masha, Surulere jihar legas.

Ya bayyana cewa wanda ake karar ya aikata laifin ne a gidan wacce take kara, Mary Kolawole, inda yake aiki a matsayin maigadi

Ya ce : “An baiwa wanda ake kara amanar makullan gidan don ya share dakin da aka ajiye sarkar.”

Dan sanda mai gabatar da karar ya mikawa kotu takardar da wanda ake kara ya amsa cewa ya aikata laifin da ake tuhumarshi.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel