'Yan arewa sun cika da murna da farinciki bayan Buhari ya yi wa Fulani makiyaya albishir mai dadi

'Yan arewa sun cika da murna da farinciki bayan Buhari ya yi wa Fulani makiyaya albishir mai dadi

Martanin fadar shugaban kasa a kan 'sa toka, sa katsin' da ta kunno kai a tsakanin shugabannin al'ummar yankin arewa da kudu a kan batun Fulani makiyayya, ta sanyaya zukatan jama'a da dama tare da saka su farin ciki.

A ranar Talata ne kungiyar dattijan arewa (NEF) ta yi kira ga Fulani makiyaya da su tattara kayansu da dukiyoyinsu su bar kudancin Najeriya matukar babu tabbacin samun tsaro a duk inda su ke zaune a yankin kudu.

Wannan kira na kungiar NEF ya jawo kungiyar 'yan asalin kabilar Igo ta mayar da martani ta hanyar umartar dukkan 'yan kabilar Igbo da ke zaune a arewa su tattara kayansu su koma gida.

Sai dai shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bukaci Fulani makiyaya da su yi watsi da kiran da kungiyar NEF ta yi musu na su dawo arewa, tare da basu tabbacin samun tsaron lafiyarsu da dukiyarsu a duk inda su ke zaune.

A Kaduna, jama'a sun bayyana wannan mataki da shugaban kasa ya dauka a matsayin wanda ya dace kuma a lokacin da ya dace, tare da bayyana cewa hakan ya nuna cewa gwamnatinsa na sauraron kiraye-kirayen jama'ar ta.

DUBA WANNAN: Ba a taba gurfanar da ni a kan badakalar biliyan N25 ba - Goje

Alhaji Kabir Boga, wani mazaunin Unguwar Sarki, a Kaduna, ya bayyana cewa shugaba Buhari ya cancanci a yaba masa saboda sauraron kiran da kungiyar dattijan arewa karkashin jagorancin Farfesa Ango Abdullahi ta yi na a bawa Fulani makiyaya tabbacin samun tsaro a duk inda su ke a kudancin Najeriya ko kuma su tattara kayansu su dawo arewa.

"Su kuniyar dattijan arewa sun damu ne saboda an fara yi wa makiyaya barazana tare da alakanta su da duk wani aikin ta'addanci a yankin kudu. Amma kalaman shugaba Buhari na tabbatar da tsaron lafiyarsu a duk inda su ke zaune a kudu, ya nuna cewa yana sauaron jama'a, ya kuma wanke kan sa daga zargin da ake yi masa cewa yana yin burus da al'amuran jama'ar da ya ke shugabanta," a cewa Boga.

Kazalika, wasu mazauna garin Kaduna irinsu Musa Zubair, mazaunin unguwar Tudun Nufawa, sun bayyana cewa dole a yaba wa kungiyar dattijan arewa da kuma fadar shugaban kasa bisa daukan matakan da suka dauka a kan Fulani makiyaya, musamman a kan tarnakin da ya taso bayan kisan diyar shugaban kungiyar Afenifere, Cif Fasoranti.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel