Wani mutum ya nemi kotu ta raba aurensa da matarsa saboda ta hanashi saduwa da ita

Wani mutum ya nemi kotu ta raba aurensa da matarsa saboda ta hanashi saduwa da ita

-Wani malamin addini ya nemi kotu ta raba aurensa da matarsa bayan sun kasance ma'aurata na tsawon shekaru 40

-Malamin mai suna Ganiyu Salami ya kure hakurinsa ne sakamakon hana shi haqqinsa na aure da matar keyi na tsawon shekaru da dama

-Matarsa Halimatu ta shaidawa kotu cewa lokacin da ya nemi saduwa da ita ta qi amincewa ba ta da lafiya ne

Wani malamin addinin musulunci mai suna Ganiyu Salami ya kai karar matarsa Halimatu Kotun Gargajiya ta Igando dake Legas, inda yake neman a raba aurensu wanda ya kai shekara 40 yanzu a sakamakon barazanar halaka shi da kuma rashin barin ya sadu da ita da matar keyi.

Salami ya shaida wa kotun cewa, matarsa wadda suka haifi yara takwas tare da ita ta dade tana hana shi haqqinsa na aure.

KU KARANTA:Wata sabuwa: Gwamnatin Uganda za ta fara bai wa shanu takardar shaidan haihuwa

Salami ya ce: “ Matata wadda ke kwana a cikin gidana, ta ci ta sha abinda ranta yaso ta wahalar dani tsawon shekara 16 inda ta hana ni saduwa da ita. Ko taba jikinta ba ta bari nayi balle ma har in kai ga saduwa da ita.

Ya cigaba da cewa: “ Aure na da Halimatu cike yake da masifu kala-kala, babu wani kwanciyar hankali a tare dani sanadiyar halayyarta. Lokuta da dama ta sha yinkurin aika ni barzahu. Ban mantawa akwai wani lokacin da muka taba samun sabani da ita, ta sa babban da na ya mani dukan tsiya.

“ Halimatu har auren ‘yata ta bayar ba tare da nasan wane ne surukin nawa ba. Burinta guda daya ne kacal. So take ta kashe ni ta gaje dukiyar da na gada daga wurin mahaifina ita da diyanta, saboda ta san matuqar ina da rai dukiyar haramunce a gareta. Ina rokon wannan kotu da ta raba aurena da wannan masifaffiyar mata domin in cigaba da rayuwa cikin kwanciyar hankali kamar yadda kowa ke yi.”

Matar tasa Halimatu ta ce: “ Tabbas na hana shi saduwa da ni amma ina da dalilina na yin hakan. Lokacin da hakan ya faru bani da lafiya ne, bayan na warke sai shi kuma ya guje ni bai saduwa da ni har ma yana kirana da suna mahaukaciya.

“ Kwatsam kawai yaje ya auro wata matar ya fita batuna. Da na kuma da ya doke shi sabani suka samu a tsakaninsu amma bani na sa shi ba kamar yadda ya fadi.”

Alkalin kotun, Adeniyi Koledoye bayan da ya gama sauraron ta bakinsu, ya dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Agusta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel