Da kyau: kamfanin Renault zai fara hada motoci a Najeriya

Da kyau: kamfanin Renault zai fara hada motoci a Najeriya

-Kamfanin Renault da kuma wani kamfanin gamayya na Najeriya, Coscharis, sunyi hadaka don fara hadawa da saida motoci kirar Renault a Najeriya.

-Kamfanin Coscharis zai fara harhada motar Renault kirar Logas da kirar Duster kuma zai fara siyar da su a cikin watan Oktoba na shekarar 2019

Kamfanin kera motoci na kasar Faransa, Renault da kuma wani kamfanin gamayya na Najeriya, Coscharis, sunyi hadaka don fara hadawa da saida motoci kirar Renault a Najeriya. Kamfanin Renault ne ya bayyana haka a yau Alhamis 18 ga watan Yuli 2019.

Fabrice Cambolive, babban mataimakin shugaban kamfanin, kuma ciyaman din kamfanin na yankin nahiyar afirika da nahiyar Gabasa ta Tsakiya ne ya bayyana haka a garin Farisa na kasar Faransa, inda ya bayyana cewa sun kara girman kamfanin zuwa Najeriya saboda mahimmancin Najeriya a nahiyar Afirika.

Ya ce : “Najeriya, inda Renault za ta kafa kamfaninta , kasa ce mai yawan mutane da ya kai miliyan 200, a saboda haka ta na da mahimmancin a nahiyar Afirika.”

Kamfanin Coscharis zai fara harhada motar Renault kirar Logas da kirar Duster kuma zai fara rarraba ma mutane ta hanyar hanyoyin da suke sayar da kayayyakinsu a duk fadin Najeriya a cikin watan Oktoba.

KARANTA WANNAN: Bashin waje na Najeriya ya kai $15.3bn a gwamnatin Buhari

A wani labari makamancin wannan, wani kamfanin kera motoci na kasar Faransa, Peugeot ya yi hadaka da kamfanin hamshakin dan kasuwa na Afirika Aliko Dangote, inda suka bayyana cewa a cikin watanni hudu na farko a shekarar 2019 za su fara hada motoci.

Mai baiwa gwamnan Kaduna shawara, Jimi Lawal ne ya bayyana ma jaridar Reuters, inda ya bayyana cewa za a kafa kamfanin a garin Kaduna kuma kamfanin zai hada motoci 3,500 a cikin shekarar farko.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel