Attajirin dan kasuwa, Alhaji Dahiru Mangal ya bada gagarumin tallafi ga yan gudun hijira

Attajirin dan kasuwa, Alhaji Dahiru Mangal ya bada gagarumin tallafi ga yan gudun hijira

-Hamshakin dan kasuwa na jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal, ya baiwa gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari kayan masarufi don a baiwa yan gudun hijira dake a jihar

-Haka zalika, hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Katsina ta bada gudunmuwar kayan abinci ga yan gudun hijira kimanin mutum 3,942

-Yan gudun hijiran sun godewa gwamnatin jihar Katsina akan irin tallafin da ta ke basu

Hamshakin dan kasuwa na jihar Katsina, Alhaji Dahiru Mangal, ya baiwa gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari kayan masarufi don a baiwa yan gudun hijira dake a jihar. Kayan sun hada da Shinkafa, Wake, Masara, Sukari, Taliya, Man Gyada, Tabarmi, Katifu da Barguna.

A lokacin da yake karbar kayan a gidan gwamnatin jihar Katsina, gwamna Aminu Bello Masari ya godewa dankasuwar a bisa tallafin da ya baiwa yan gudun hijiran.

Gwamnan ya bayyana cewa, Alhaji Dahiru Mangal ya dade yana bada tallafi ga kungiyoyi da asibitoci da gidan marayu da musakai, da raban abinci a lokacin watan Ramadan ga kowane mabukaci. Gwamnan yayi fatan alkhairi ga dan kasuwar.

Haka zalika, hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Katsina ta bada gudummuwar kayan abinci ga yan gudun hijira kimanin mutum 3,942 da suka yadda zango a makarantar firamare ta Nuhu Model da ke a karamar hukumar Kankara.

Da ya ke gabatar da kayan, shugaban hukumar, Alhaji Babangida Nasamu wanda daraktan bincike na hukumar Alhaji Iliya Ibrahim ya wakilta, ya bayyana cewa kayan sun hada da buhunan Masara 60 buhunnan Gero 50 da buhu 60 na Shinkafa da sauransu.

Alhaji Babangida Nasamu yayi ta’aziyya ga mutanen da suka rasa yan uwansu sakamakon hare haren da aka kai.

KARANTA WANNAN: Dalar da kace zaka bai wa 'yan kwallon kafa idan sunyi nasara ka taimaka mana mu masu jinya - Sakon Uwani ga Dangote

A jawabin godiya shugaban kwamitin riko na karamar hukumar wanda ya samu wakilcin mataimakinsa Alhaji Umar Yahaya Girbobo ya godewa gwamna Masari akan irin gudunmuwar da yake baiwa yan gudun hijaran.

Yan gudun hijiran sun godewa gwamnatin jihar Katsina akan irin tallafin da ta ke basu, sun kuma yi kira ga gwamnatin da ta taimaka wajen ganin an kawo karshen matsalolin tsaro a garuruwansu ta yadda za su samu su komawa gidajensu.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel