Ku bar aibata kabilar Fulani – Matthew Kukah

Ku bar aibata kabilar Fulani – Matthew Kukah

-Matthew Kukah ya jawo hankalin masu hantarar Fulani kan cewa su bari kada abin ya haifar da rikicin da ba'a san ranar tsayawarsa ba

-Yayi wannan kiran ne wurin wani taro na musamman da NOUN ta shirya domin fadakar da al'umma a kan rashin fa'idar kirkirar rikicin kabilu

Bishop Matthew Kukah na Cocin Katolika dake Sokoto yayi gargadi ga masu aibata makiyaya musamman wadanda suka fito daga kabilar Fulani, inda ya ce cigaba da hantararsu kan iya haifar da barkewar rikici.

Kukah yayi wannan gargadin ne ranar Talata wurin wani taro na musamman da National Open University of Nigeria (NOUN) ta shirya domin tunatarwa kan abubuwan da kalaman batanci kan iya haifarwa.

KU KARANTA:Kar ku bari El-Zakzaky ya mutu a gidan kaso, Falana ya gargadi gwamnati tarayya

Biyo bayan jerin hare-haren da sukayi ta aukuwa cikin kwankin nan, mutane da dama na danganta wannan aiki da cewa Fulani ke yinsa. Irin wannan abin ne idan bamu manta ba ya janyo yaqin basasan Najeriya da kabilar Igbo tsakanin 1967 zuwa 1970.

A cewar Kukah: “ Idan yau Fulani ne to jiya kuma Igbo ne.” Da yake korafi a kan gogawa Fulani kadai bakin fenti bisa hare-haren da ake zargin makiyaya ne keyi a yau, Kukah ya ce mene ne zai sa a ware Fulani kadai a daura masu laifi bayan muna da wasu kabilu na daban a kasar nan?

“ Duk sanda na bude fasfo dina zan tarar da akwai tamburan kasar nan da dama, na farko doki ne da dagi. Abu na gaba shi ne bayani a kan karan kaina. Shafi na gaba kuwa dauke yake da dutsen Zuma rock da wasu ‘yan kabilar Tibi na rawarsu ta gargajiya. Da naga hotonsu na tambayi kaina, shin wa ya basu damar sanya Tibi a nan wurin?

“ A shafin dake gaban wannan kuwa wani bafulatani na gani yana kiwon shanunsa. Abinda yawancinmu keyi na kiran Fulani da sunan ‘yan ta’adda kuskure ne babba bai kamata mu tsanesu ba kada abin ya haifar da rikici mai tsanani.” Inji Matthew Kukah.

A karshe ya yi kira ga masu mulki da su tashi tsaye domin magance matsalar bambancin kabila da ake samu a kasar nan domin samar da cigaban zaman lafiya.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel