Kamfanin Total ya kaddamar da ayyuka 10 a arewacin Najeriya

Kamfanin Total ya kaddamar da ayyuka 10 a arewacin Najeriya

-Kamfanin man fetur na Total ya bayyana cewa ya kashe Naira biliyan daya wajen gudanar da ayyuka 10 a jihohi takwas a arewacin Najeriya

-Mataimakin daraktan kamfanin ya bayyana cewa ayyukan na da zummar inganta ilimin fasaha, lafiyar mata da kanan yara, samar da tsaftataccen ruwan sha da kuma tsaftace muhalli

Kamfanin man fetur na Total ya bayyana cewa ya kashe Naira biliyan daya wajen gudanar da ayyuka 10 a jihohi takwas a arewacin Najeriya don bayar da gudunmuwarshi don inganta rayuwar al’umma.

Da yake magana a lokacin da ake bude ayyukan tare da hannanta su ga al'umma, mataimakin babban daraktan kamfanin, Engr Ahmadu Kida Musa, ya bayyana cewa kamfanin ya gudanar da ayyukan ne a matsayin hakkin da ya ke akanshi ya ba al’umma.

Ya bayyana cewa ayyukan na da zummar inganta ilimin fasaha, lafiyar mata da kanan yara, samar da tsaftataccen ruwan sha da kuma tsaftace muhalli.

Ya bayyana cewa “An zabi wuraren da aka gudanar da ayyukan a tsanake don inganta rayuwar yan gudun hijirah musamman na yankin arewa maso gabas a kasar nan. Ayyukan sun kuma yi daidai da muradun majalisar dinkin duniya”

Ya bayyana cewa mafi yawan ayyukan an sama masu na’urar wutar lantarki mai anfani da hasken rana saboda bashi bukatar kudade sosai wajen kula dashi kuma mutane za su iya yin anfani dashi cikin sauki.

Da yake bayyana adadin kudin da ayyukan suka lashe, ya ce “Ayyukan da muke budewa yau, an gina su ne akan kudi kusan Naira biliyan daya.”

Ya bayyana cewa ayyukan sun hada da gine gine, kayayyakin makarantaun koyan sana’o’i, kayayyakin dakin gwaje gwaje na kimmiya, da kayayyakin na’ura mai kwakwalwa.

KARANTA WANNAN: Haka Allah ke lamarinsa: Ta samu mijin aure da kyautar kujerar Makkah saboda soyayyar da take yiwa Abba Gida-Gida

Ta fannin inganta lafiya, ya ce kamfanin ya gina asibitoci guda hudu na mata da kananan yara a arewa maso gabas don taimakwa mata da kananan yara da suka sha fama da ta’addanci a arewa maso gabas.

Ya bayyana cewa an gina santar duba nonuwan mata a garin Anka dake a jihar Zamfara, an yi aikin ruwa a Offa dake a jihar Kwara, da Birnin Kebbi na jihar Kebbi. An samar da dakin gwajegwajen kimmiya a jihar katsina da kuma dakin na’ura mai kwakwalwa a jihar Bauchi.

Haka zalika an gina santar duba lafiyar mata da kananan yara a Bama dake a jihar Borno

Da yake mika sakon godiya, komishinan ilimi na jihar Sokoto, Farfesa Bashiru Garba ya godewa kamfanin da abokan huldarshi ya kuma yi kira ga sauran kamfanoni da su yi koyi da kamfanin na Total.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel