Rashin Tsaro: Sarkin Katsina ya umurci hakimai da su kafa kwamitocin tsaro

Rashin Tsaro: Sarkin Katsina ya umurci hakimai da su kafa kwamitocin tsaro

-Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya umurci duka hakimai 45 dake a karkashin masarautar Katsina da su kafa kwamitocin tsaro

-Sarkin ya bayar da umurnin ne a jiya Talata 16 ga watan yuli 2019 a lokacin da yake ganawa da hakiman na sa a fadarsa dake a Katsina

-Sarkin yayi kira ga mutane da su rinka isar da bayanai ga shuwagabannin gargajiya dangane da duk wasu mutanen da basu yadda da su ba

Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman ya umurci duka hakimai 45 dake a karkashin masarautar Katsina da su kafa kwamitocin tsaro don taimakawa wajen magance matsalolin tsaro da ake fama da su a wasu wajaje a masarautar.

Sarkin ya bayar da umurnin ne a jiya Talata 16 ga watan yuli 2019 a lokacin da yake ganawa da hakiman na sa a fadarsa dake Katsina.

KARANTA WANNAN: Kyawun tafiya dawowa: Bayan shekaru 12 da rasuwar mijinta jaruma Hafsat Shehu ta dawo harkar fim

Ya bayyana cewa:“Hakimai su hada kai da dagattai don su rinka samar da bayanai ga jami’an tsaro a garuruwansu. Su baiwa jami’an tsaro duk wata gudunmuwa da suke bukata don ganin sun samar da tsaro a yankunan.”

“Masarautar Katsina za ta yi duk iya kokarinta don ganin an magance matsalolin tsaro dake addabar yankunanta.”

Sarkin yayi kira ga mutane da su rinka isar da bayanai ga shuwagabannin gargajiya dangane da duk wasu mutane da basu yadda da su ba. Ya bayyana cewa:“Hakkin kowa ne ya isar da bayanai dangane da duk wasu mutanen da bai yadda da su ba ga hakimai da masu gari don a dauki matakin da ya dace.”

Ya kara da cewa: “Babu wani bakon da zai sauka a gari ba tare da izinin hakimi ko mai gari ba da ke a karkashin masarauta ta.”

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel