Ganduje ya cika alkawarin da yayi, ya ba Zainab da Ibrahim N6m

Ganduje ya cika alkawarin da yayi, ya ba Zainab da Ibrahim N6m

-Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya cika alkawarin da yayi na cewa zai ba Zainab Aliyu da Malam Ibrahim Abukarar Naira miliyan uku kowannensu sakamakon sharrin da aka yi masu na daukar kwayoyi zuwa saudiyya.

-Kwana daya bayan dawowar Zainab Najeriya, gwamna Abdullahi Ganduje ya karbi Zainab a gidan gwamnatin kano inda ya yi alkawarin cewa zai biya su diyyar Naira miliyan uku uku da ita da Malam Abubakar

A jiya Litinin 15 ga watan Yuli 2019, gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya cika alkawarin da yayi na cewa zai ba Zainab Aliyu da Malam Ibrahim Abubakar Naira miliyan uku kowannensu sakamakon sharrin da aka yi masu na daukar kwayoyi zuwa saudiyya.

Da yake mika masu takardar bankin, sakataren gwamnatin jihar, Usman Alhaji, ya ce “Gwamnatin tarayya da ta jihar Kano sun yi kokari sosai na ganin cewa an sako mutane biyu da kasar Saudiyya ta kama da laifin da basu da masaniya a kanshi.”

Malam Abubakar, ya godewa duka mutanen da suka taimaka wajen ganin cewa an sako su daga gidan kaso na kasar Saudiyya. Haka zalika yayi godiya ga gwamnatin jihar da ta taimaka masu da wadannan kudaden.

Idan za a iya tunawa, a ranar 14 ga watan Mayu 2019, Legit.ng ta ruwaito cewa Zainab Aliyu, daliba yan Najeriya da ake zargin ta da yin safarar kwayoyi zuwa kasar Saudiyya ta dawo gida Najeriya bayan shafe watanni hudu a tsare a kasar Saudiyya.

KARANTA WANNAN: Allura zata tono garma: Hon. Abdulmumini Jibrin yayi barazanar tona yadda aka yi magudin zaben 2019 a jihar Kano

An saki Zainab Aliyu da Malam Abubakar bayan da gwamnatin tarayya ta gudanar da bincike ta kuma tabbatar da cewa basu da laifi. Zainab ta samu karba daga wajen dubunnan mutane a filin kasa da kasa na malam aminu Kano.

A ranar 15 ga watan Yuli 2019, kwana daya bayan dawowar Zainab Najeriya, gwamna Abdullahi Ganduje ya karbi Zainab a gidan gwamnatin kano inda ya yi alkawarin cewa zai biya su diyyar Naira miliyan uku uku da ita da Malam Abubakar wanda a lokacin yana a hannun jakadun Najeriya na kasar Saudiyya.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel