Rundunar yan sanda ta ce ba a kaima shaidun Atiku hari a Zamfara ba kamar yadda yayi ikirari

Rundunar yan sanda ta ce ba a kaima shaidun Atiku hari a Zamfara ba kamar yadda yayi ikirari

-Rundunar yan sanda ta karyata ikirarin da akeyi na cewa yan ta’adda sun kaima shaidun Atiku hari akan hanyarsu ta zuwa Abuja don su bayar da shaida

-Jami’in hulda da jama’a na rundunar ya ce ba a taba samun harin da aka tabayi ga mutanen da ke tafiya akan babban titi na jihar ba

-Rundunar ta kuma yi kira ga gidajen yada labarai da su rinka tabbatar da gaskiyar labari kafin su yada shi ga duniya

Rundunar yan sanda ta jihar Zamfara ta karyata ikirarin da akeyi na cewa yan ta’adda sun kaima shaidun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyara PDP, Alhaji Atiku Abubakar hari akan hanyarsu ta zuwa Abuja don su bayar da shaida a tuhumar da Atiku ke yi ma Shugaba Buhari.

Rundunar ta karyata zancen da shaidun ke yi na cewa an kai masu hari a Zamfara, wanda hakan ya sanya suka fice daga motocinsu suka ruga cikin daji, wanda hakan ya kawo tsaiko a tafiyar da suke yi na zuwa bada shaida a kotu.

A jawabin da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Muhammad Shehu ya fitar, rundunar, ta bayyana cewa “Ya zama wajibi mu fadi karara cewa a duk kidayar da akayi na hare haren da yan ta’adda ke kaiwa a Zamfara, ba a taba samun harin da aka tabayi ga mutanen da ke tafiya akan babban titi na jihar ba.”

Ya kara da cewa “Tun daga lokackin da aka fara yin sulhu da sasanci a jihar, ta’addanci da sace sacen mutane a jihar ya ragu da kusan kashi 98, wanda hakan ya sanya yanzu ake zaune lami lafiya a jihar.”

KARANTA WANNAN: Wasu Gwamnonin da su ka sauka daga mulki su na neman kujerun Minista

Shehu ya bayyana cewa sun yi nasarar da ba a taba yi ba bayan da suka ceto fiye da mutane 100 da yan bindiga sukayi garkuwa da su tsawon watanni, sakamakon shirin sulhu da komishinan yan sanda na jihar Usman Nagoggo ya shigo da shi.

Ya bayyana cewa “A sabi da haka, hukumar yan sanda na karyata labarin gaba dayanshi saboda saboda labarin na so ya lalata kokarin gwamnatin jihar da rundunar yan sanda na ganin an samu zaman lafiya don ci gaban jihar.”

Rundunar ta kuma yi kira ga gidajen yada labarai da su rinka tabbatar da gaskiyar labari kafin su yada shi ga duniya.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel