Dalibai 11 na jami’ar Unilorin sun suma a dakin jarabawa

Dalibai 11 na jami’ar Unilorin sun suma a dakin jarabawa

-A kalla dalibai 11 na Uilorin suka suma a ranar Juma’a a lokacin da ake rubuta jarabawar zangon karatu na biyu

-Wata majiya ma cewa tayi dalibi guda daya ya rasa ranshi a lokacin da ake kokwar

-Mai magana da yawun jami’ar, Kunle Akogun ya ce ba gaskiya bane labarin da ake yadawa cewa wani dalibi ya rasa ransa

A kalla dalibai 11 na jami’ar Ilorin (Uilorin) suka suma a ranar Juma’a 12 ga watan Yuli 2019 a lokacin da ake rubuta jarabawar zangon karatu na biyu.

Lamarin ya faru ne lokacin da daliban ke kokowar samun wajen zama a dakin jarabawar. Wata majiya ma ta bayyana cewa dalibi guda daya ya rasa ranshi a lokacin da ake kokowar. Amma shugabannin jami’ar sun musanta labarin.

Majiyar ta bayyana cewa “Lamarin ya janyo anyi take take a lokacin da daliban Kemistiri da na koyarwa suke kokowar samun wajajen zama 300 da ke a dakin jarabawar.”

Ya kara da cewa “Rashin kula daga hukumar makaranta ne ya jawo haka. Yawan daliban kemistiri da za su yi anfani da dakin jarabawar sun kai 2000 haka kuma daliban bangaren koyarwa sun kai su 5000. Amma duk da haka hukumar makarantar na so a kammala jarabawa a ranar 26 ga watan Yuli 2019 a kuma fara jarabawar samun gurbin karatu a ranar 27 ga watan Yuli".

Da yake bada bayani akan afkuwar lamarin, mai magana da yawun jami’ar, Kunle Akogun ya ce ba gaskiya bane labarin da ake yadawa. Babu dalibin Unilorin da ya rasa ranshi a wajen dakin jarabawa na CBT a ranar Juma’a.

Ya bayyana cewa‘'Gaskiya ne wasu dalibai sun suma saboda gajiya a lokacikn da akayi take take a dakin jarabawa na CBT saboda rashin hakurin wasu dalibai da suke kokarin su riga wasu shiga dakin jarabawar wanda hakan ya sanya suka fara ture ture. Wannan ne ya sanya kusan dalibai 10 suka gaji suka suma.”

KARANTA WANNAN: Ambaliyar ruwa ta mamaye wasu makarantu a Jigawa

An yi maza an kaisu asibitin makaranta don a duba su. Hudu daga cikinsu ma nan take aka sallame su don su ci gaba da rubuta jarabawarsu, shida daga ciki kuma aka cigaba da duba su. An sallami hudu a ranar Juma’a da marece sauran biyun kuma aka sallame su da safiyar ranar Asabar.

Ya bayyana cewa jami’ar ba ta ji dadin afkuwar lamarin ba, inda kuma yayi kira ga daliban jami’ar da su sanya hakuri a lokacin rubuta jarabawa. Ya bayyana cewa an shirya jarabawar ta na’ura mai kwakwalwa (CBT) ta yadda kowanne dalibi zai rubuta cikin sauki.

Daga karshe ya kammala da cewa “Muna yi ma kowa fatan alkhairi a jarabawar.”

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel