An kama wani malamin makaranta dumu-dumu yana lalata da dalibansa yara mata uku
-An kama malamin makaranta dumu-dumu yana keta haddin dalibansa mata uku 'yan kasa da shekara 10
-Mutane da ke wucewa ta kusa da ajin da malamin ke aikata wannan aika-aika ne suka jiyo kukan yaran suka shiga domin kai masu dauki
-Malamin ya fadi a bayaninsa cewa ba karo na farko ba kenan da yake aikata irin wannan laifin kuma ya sha zuwa wurin 'yan sanda a kan wannan aiki
Wani malamin makaranta mai shekaru 21, Moshood Abdul ya shiga hannun ‘yan sanda a Ogijo jihar Ogun bayan an kama shi dumu-dumu yana lalata da daliban makarantarsa uku.
Shi dai wannan mutum yayi amfani ne da kudi N100 inda ya bai wa ko wace daliba daya daga cikinsu daga bisa ni ya kai su lungun wani aji a makarantar domin biyan buqatarsa.
KU KARANTA:Zaben 2019: Yau Atiku zai gabatar da bidiyo matsayin shaida a kotu
Mutane masu wuce wa ta kusa da hanyar ne suka jiyo kukan yaran suka afka cikin ajin inda suka kama Moshood dumu-dumu yana aikata lalata da yaran.
Ba tare da bata wani lokaci ba aka miqa shi hannun yan sanda yankin Ogijo na jihar Ogun domin gudun aukuwar wannan mummunan abu a tattare da shi.
Wata majiyar ta shaidawa jaridar The Nation cewa: “ Gaba daya yaran uku, babu wacce ta haura shekara goma da haihuwa kuma dukkaninsu daliban makarantar da malamin ke koyarwa ne.”
Haka zalika, mutumin ya bada jawabin cewa: “ Ba wannan bane karonsa na farko da ya fara aikata laifin. Inda ya ce ya saba yi kuma an sha kama shi ana kai shi wurin yan sanda a kan laifin.”
A daidai lokacin da muke hada wannan rahoton bamu samu jin ta bakin kakakin yan sandan jihar ba wanda muka so yayi mana tsokaci a kan wannan al’amari.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng