Tambayoyi akan shin shugaba Buhari ya iya turanci ta dabaibaye zaman kotun zabe

Tambayoyi akan shin shugaba Buhari ya iya turanci ta dabaibaye zaman kotun zabe

-Tambayoyi akan ko shugaba Buhari ya iya magana da turanci ne suka dabaibaye zaman kotun zabe da akayi a jiya Talata 9 ga watan Yuli

A zaman da akayi na ranara Talatan, shaidu biyu ne na masu tuhuma suka gabatar da shaidunsu

-Tambayoyin na da alaka da ikirarin da masu kara ke yi na cewa shugaba Buhari bashi da cikakken ilimin da zai nemi mukamin shugaba kasa.

Tambayoyi akan ko shugaba Buhari ya iya magana da turanci ne suka dabaibaye zaman kotun zabe da akayi a jiya Talata 9 ga watan Yuli, inda jam’iyyar PDP da dan takararta na mukamin shugaban kasa a zaben 2019 suke kalubalantar nasarar shugaba Buhari.

Shaidu biyu ne na masu tuhuma suka gabatar da shaidunsu inda lauyoyin shugaba Buhari da jam’iyyar APC, Wole Olanipekun (SAN) da Lateef Fagbemi suka yi masu tambayoyi.

Tambayoyin na da alaka da ikirarin da masu kara ke yi na cewa shugaba Buhari bashi da cikakken ilimin da zai nemi mukamin shugaba kasa.

Shaidan masu tuhuma na farko a ranar Talatan, wanda kuma shine na bakwai da masu tuhuma suka gabatar, shine jam’in tattara sakamakon zabe na PDP a jihar Niger, Tanko Beche, wanda ya bayyana cewa shi lauya ne.

An tambaye shi ko yaga yadda shugaba Buhari da Atiku Abubakar suka gudanar da Kamfen dinsu, yace ya kalli yadda shugaba Buhari ya gudanar da nashi a talabijin sa’annan kuma yace da shi aka gudanar da na Atiku.

An tambayeshi ko yana da masaniya cewa shugaba Buhari da turanci ya gudanar da kamfen dinshi musamman a kudancin kasarnan, ya ce shi bashi ne zai fadi yadda aka gudanar da kamfen din ba.

KARANTA WANNAN: Buhari ya aika ma majalisa sunayen mutane 5 da zai nada muhimman mukamai

An tambayeshi ko a wane aji yake a tsakanin shekarar 1983 zuwa 1985, ya ce lokacin ya na makaranar Firamare.

Daga nana sai aka tambayeshi ko wanene shugaban kasa a wannan lokacin inda ya ce “Tarihi ya nuna mani cewa Muhammadu Buhari ne”

An tambayeshi ko yana da masaniya cewa shugaba Buhari na yin jawabi ga kasa da turanci a lokacin, ya ce “Dama shugaban kasa da turanci ya kamata yayi magana.”

Shaida na gaba bayan Beche, shine shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina, Alhaji Salisu Yusuf Majigiri, wanda ya bayyana cewa shi ne kuma jami’in tattara sakamako na jam’iyyar PDP a jihar Katsina. Ya bayyana cewa an haifeshi a shekarar 1963.

Ya bayyana cewa yana da masaniya cewa shugaba Buhari ne shugaban kasa daga 1983 zuwa 1985. An tambayeshi ko a wanne aji yake a lokacin, ya masa cewa “Ina aji uku na makarantar sakandare.”

An tambayeshi ko yasan cewa a lokacin shugaba Buhari na yin jawabi da turanci, sai yace “Kila lokacin ina kauye.”

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel