Shugabannin kananan hukumomi sun tuhumi gwamnatin jihar Zamfara da tauye masu kudade

Shugabannin kananan hukumomi sun tuhumi gwamnatin jihar Zamfara da tauye masu kudade

-ALGON reshen jihar Zamfara ta yi ikirarin cewa gwamnatin jihar na tauye masu kudadensu da aka turo daga gwamnatin tarayya

-Mai magana da yawun kungiyar ya bayyana cewa gwamnatin na yin haka ne saboda ba jam'iyyarsu daya ba

-Babban darakta akan harkokin gidajen jari na gwamna Matawalle ya musanta maganar in da ya bayyana cewa shugabannin kananan hukumomin na da wata manufa a ransu

Kungiyar shuwagabannin kananan hukumomi reshen jihar Zamfara (ALGON) ta yi ikirarin cewa gwamnatin jihar Zamfara na tauye masu kudadensu da aka turo daga gwamnatin tarayya, duk da umurnin da shugaban kasa ya bayar cewa a hannanta ma kananan huumomi kudadensu.

Da yake zantawa da manaima labarai, mai magana da yawun kungiyar kuma shugaban karamar hukumar Maradun, Alhaji Ahmed Abubakar, yayi ikirarin cewa gwamnatin jihar ta karya umurnin da shugaban kasa ya bayar.

Ya ce "Munyi mamaki matuka da wakilan gwamnati suka fada mana cewa baya ga kudaden da aka saba badawa na albashin ma'aikata da sauran kudaden da ya wajabta a cire, an basu umurni da su ba kowanne shugaban karamar hukuma Naira miliyan biyar da zai gudanar da mulkin karamar hukumar tsawon kwanaki 30 masu zuwa."

KARANTA WANNAN: Elisha Abbo: Hadimar Buhari tace lallai sai dai a tura sanatan gidan yari

"Haka ya tabbatar da zargin da mukeyi na cewa gwamnatin jihar nan karkashin jagorancin PDP na kokarin ta sauke duka shugabannin kananan hukumomi 14 saboda ba jam'iyyar mu daya ba."

Ya bayyana cewa duka shuwagabannin kananan hukumomin da aka zaba karkashin tutar jam'iyyar APC za su kai gwamnatin jihar kara idan ta sake yin kokarin hana su kudadensu.

Da yake maida martani game da zargin, babban darakta na al'amurran gidajen jarida, Alhaji Yusuf Idris ya ce "An gayyaci shuwagabannin kananan hukumomi zuwa wajen taron duba asusun ajiya na hadaka da akeyi duk wata wata amma suka ki halartar taron."

"Hakan ya nuna cewa shugabannin kananan hukumomin na da wata manufa saboda mai girma gwamna matawalle ba shi da hannu a taron illa ya tabbatar da cewa anyi abun da ya dace."

Ya kara da cewa "Gwamna Matawalle ya sha fadi cewa zai tafida kowa a cikin gwamnatinsa kuma zai ba kowa dama iri daya don ganin an tafiyar da jihar gaba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel