Mutumin da matarsa ta dabawa wuka ya samu lafiya, ya nunawa bidiyon tsairaci da matarsa ke tura wa samarinta

Mutumin da matarsa ta dabawa wuka ya samu lafiya, ya nunawa bidiyon tsairaci da matarsa ke tura wa samarinta

-Sa'id Hussain wanda matarsa ta yi yinkurin aika wa barzahu ya fallasa asirinta

-Sa'id ya fadi cewa matarsa ta kasance ne tana mu'amala da samarin duk cewa ita matar aure ce lamarin da yakai har hotunan tsaraici take tura masu

-A cewar Hussain iyayen matar tasa duk sun san da wannan batun saboda a lokacin da ya samu wani bidiyo irin na tsaraici da take aika wa samarin nata ya aika wa iyayen da shi

Sa’id Hussain wanda matarsa Fatima Musa mai shekaru 21 ta kusa aika shi lahira ta hanyar daba masa wuka ya farfado a yayin da ya bayyana gaskiyar yadda lamarin ya faru.

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 1:30 na daren Asabar 22 ga watan Yunin 2019, a gidan ma’auratan wanda ke Unguwar Mai kalwa, Na’ibawa quarters a karamar hukumar Kumbotson jihar Kano kamar yadda majiyar Daily Focus ta ruwaito.

KU KARANTA:Gwamnatin Kano ta bada kwangilar N730m domin yin gini a Asibitin Buhari

Iyalan matar sun yi ta yinkurin kare diyarsu ta hanyar wanke ta daga zargi inda suke yada labarin cewa mijin ya lakada matar dukan tsiya. Wannan ya sanya aka cigaba da yada wani bidiyo mai nuna matar dauke da rauni a fuska domin a ga laifin mijinta.

Amma sai dai a wata hira da ya shirya da manema labarai a gidansa, Hussain ya fadi cewa matarsa ta kasance ta na ha’intarsa kuma shi bai bugeta ba kamar yadda ake yada wa.

Ga abinda Hussain ya ce: “ Da kaina na kama matata tana daukar rawan da take da wayarta domin ta tura wa samarinta. Dana tadda wannan al’amari na garzaya domin sanar da mahaifiyarta inda ta roke ni da kada na fada wa kowa zata yi maganin matsalar.

“ Na taba yin magana da wani saurayinta na kalubalance shi cewa bai san da matar aure yake magana bane, ya ce da ni bai sani ba. Yanzu haka ina dauke da saqo mai daukar murya da su kayi ta musaya ita da shi kusan guda 30.

“ Har wa yau, akwai hotuna masu nuna tsaraici da kuma bidiyo da take dauka da wayarta domin tura wa samarinta. Duk ina dauke da su a matsayin shaida kuma na turawa iyayenta ta hanyar WhatsApp."

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel