Nukuliya: Kasar Iran za ta tattauna da Kasar Faransa

Nukuliya: Kasar Iran za ta tattauna da Kasar Faransa

-Emmanuel Macron zai tattauna da Shuagaban Iran Hassan Rouhani domin shawo kan matsalar nukilyar Iran wadda ke kasa a halin yanzu

-Kasar Faransa da Iran na shirin yin wannan tattaunawar ne domin samun maslaha ta yadda za'a guje ma cigaba da saba yarjejeniyar shirin nukiliyar 2015

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron ya zanta da takwaransa na Iran, Hassan Rouhani ta wayar tarho inda ya bayyana damuwarsa kan matsalar da Iran din za ta iya fuskanta idan ta cigaba da saba yarjejeniyar da aka yi a 2015 kan shirin nukiliyar.

Shugabannin guda biyu sun bayyana cewa a cikin mako mai zuwa za suyi kokarin duba sharuddan yarjejeniyar domin sabunta tattaunawar da aka yi bisa yarjejeniyar.

KU KARANTA:Buhari ya tashi daga Abuja zuwa Nijar domin halartar taron AU

Kasar Iran din ta ce, a ranar Lahadi za ta yi bayani kan irin cigaban da take samu na kara inganta sinadarin Uranium dinta wanda yin haka zai saba wa ka’idojin da aka gindaya cikin yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015.

Har ila yau, Iran na da bukatar kasashen Turai da su nemi hanyoyin da za su bi domin rage tasirin takunkumin da Amurka ta kakaba mata wanda ya shafi tattalin arzikinta.

Rahotanni daga Faransa na nuna cewa, Mista Macron zai cigaba da tuntubar bangaren Iran da sauran abokan hulda na kasashen waje domin rage fargabar dake akwai a kasa yanzu.

A halin yanzu dai, a iya cewa yarjejeniyar shirin nukiliyar Iran na cigaba da zagwanyewa in banda dan abinda ya rage kalilan wanda ya hana ta wargajewa baki daya.

A bana dai ana ta samun sabani tsakanin Amurka da Iran tun bayan da Amurka ta zargi Iran da laifin kai wa jiragen mai biyu hari a mashigar tekun Oman.

Bayan nan kuma, Iran din ta harbo wani jirgin kasar Amurka a mashigar Tekun Hormuz, abinda Shugaba Trump ya kira “babban kuskure” wanda yake ganin kasar Iran din ta yi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel