Ai ga irinta nan: An daure Ahmed tsawon watanni saboda yada hotunan batsa

Ai ga irinta nan: An daure Ahmed tsawon watanni saboda yada hotunan batsa

-Kotu ta kama wani Ahmed Oladimeji da laifin yin amfani da na'ura mai kwakwalwa wajen tura hotunan batsa

-Hakan ya biyo bayan da hukumar EFCC ta kai shi kara a bisa zarginsa da aikata laifin

-Kotun ta kuma umurci da a kwace kayayyakin da ya ke amfani da su wajen tura hotunan

A jiya Alhamis 4 ga watan Yuli 2019 ofishin hukumar hana cin hanci da rashawa (EFCC) dake a Ibadan, yayi nasara, bayan da mai shari’a Ibrahim Watilat ta babbar kotun gwamnatin tarayya dake a Abeokuta, jihar Oyo, ta kama wani Ahmed Oladimeji da laifin da hukumar ke tuhumarsa da shi.

An kama Ahmed Oladimeji da laifin tura hotunan batsa da na tsiraici ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa.

Laifin ya saba ma sashe na 24 (1)(a) da sashe na 24 (1)(b) na dokar hana laifi ta yanar gizo wadda akayi a shekarar 2015.

Ahmed ya amsa laifin sa bayan da lauyanshi da hukumar suka shiga yarjejeniya, wanda hakan ya sanya hukumar ta rage laifin da ta take tuhumarsa da shi.

KARANTA WANNAN: Main Labarai LABARAISIYASA An gano yarjejeniyar da aka kula tsakanin Goje da Shugaba Buhari kafin ya janye takararsa

Baya ga wata hudu da zaiyi a gidan yari sakamakon kama shi da laifin, kotun ta kuma umurce shi da ya mayar da kudin kasashen waje da ya karba daga hannun wadanda laifin nashi ya shafa.

Kotun ta kuma bada umurnin a kwace duka kayayyakin da aka samu a hannunshi a lokacin da ake gudanar da bincike da suka hada na’ura mai kwakwalwa kirar Toshiba, wayar hannu kirar Iphone 6 da kuma wata wayar kirar Tecno KA. Kotun ta umurci da a mallaka ma gwamnatin tarayya kayayyakin.

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel