Yajin aiki: Ma’aikatan gwamnatin tarayya sun ba da wa’adin kwana 7

Yajin aiki: Ma’aikatan gwamnatin tarayya sun ba da wa’adin kwana 7

-Kungiyar Manyan ma’aikatan gwamnati (ASCSN) ta ce zata shiga yajin aiki

-Kungiyar ta ce zata shiga yajinn aikin ne saboda hukumar inshora (NAICOM) ta karya yarjejeniyar da suka kulla cikin watan August 2018

-Kungiyar ta ce ta ba NAICOM wa’adin kwana bakwai ta cika yarjejeniyar da suka kulla

Manyan ma’aikatan gwamnati karkashin kungiyar manyan ma’aikatan gwamnati (ASCSN) ta ce za ta shiga yajin aiki sakamakon karya dokar ma’aikatan gwamnati da yarjejeniyar da suka kulla da hukumar inshora ta Najeriya (NAICOM).

ASCSN ta ce sharuddan yarjejeniyar da aka rattafa ma hannu a ministirin kwadago a cikin watan Agusta na 2018, sun hada da samar da kudin alawus na man fetur da dizil, da kuma ba sauran ofisoshi mahimmanci.

Kungiyar ta ce zata shiga yajin aikin idan hukumar ba ta zartar da sharuddan yarjejeniyar ba nan da kwana bakwai.

KARANTA WANNAN: Sojoji sun hallaka yan bindiga 24 a Kaduna, Kano da Neja

A jawabin da sakataren kungiyar, Isaac Ojemheken, ya sanyawa hannu, ASCSN, ta ce “Muna a matse shi ya sanya muke sanar maku cewa mambobin kungiyar ASCSN ta yi taro a Abuja a ranar 24 ga watan Yuni 2019, kuma an cimma matsaya cewa a ba hukumar inshora wa’adin kwana bakwai don ta tabbatar da yarjejeniyar da ta kulla da kungiyar mu.”

“Ya zama dole mu sanar cewa ASCSN ba ta da laifi idan har aka shiga yajin aiki sakamakon rashin biya ma yan kungiyar bukatunsu cikin kwana bakwai.”

“Haka zalika, ya zama dole mu sanar cewa babban sakataren ministirin kwadago da aiki, babban sakataren ministirin kudi, babban daraktan yan sandan cikin gida (DSS), babban sifeton yan sanda, da shugaban hukumar inshora duk sun sanya hannu a wannan takarda."

“Muna cikin rashin jin dadi muke bayyana maku cewa bayan shekara biyu da cimma yarjejeniyar farko a ranar 26 ga watan Satumba 2017, hukumar ta inshora ta ki tabbatar da yarjejeniyar da gan gan duk da rokon da aka yi masu."

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel