Hukumar ‘yan sanda ta fito da sabon tsari domin kawar da ‘yan bindiga, inji DIG

Hukumar ‘yan sanda ta fito da sabon tsari domin kawar da ‘yan bindiga, inji DIG

-Hukumar 'yan sanda ta kirkiro wani sabon tsarin murkushe 'yan bindiga

-Mataimakin sufeton yan sandan Adulmajid Ali shi ne ya bada wannan bayanin a Sokoto

-Abdulmajid ya ce za su bi sahun 'yan bindigan har wuraren da suke gudanar da ayyukansu domin tarwatsa su

Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta fito da wani tsari na musamman domin kawo karshen masifar ‘yan bindiga a kasar nan. Mataimakin sufeton ‘yan sandan, Abdulmajid Ali ne yayi wannan bayani a jihar Sokoto.

Da yake jawabi ga jami’an yan sandan da kuma shugabannin kungiyar Miyetti Allah, Abdulmajid ya ce: “ Kwanan nan jami’an ‘yan sanda za su fara shiga cikin dajin da ‘yan bindiga ke aiki a ciki, saboda mun fara samun kayan aiki daga wurin gwamnati.”

KU KARANTA:Gwamnatin tarayya za ta fara biyan tsoffin ma’aikatan Nigerian Airways

“ Mun fito da wani sabon tsari na musamman. Zamu yaki ta’addancin ‘yan bindiga har sai mun ga bayansa. Zamu shiga Isa domin mu tabbatar da cewa mun tsaftace ta daga miyagun ‘yan ta’adda.”

“ Muna da jajirtattu kuma hazikan jami’ai wadanda za su iya magance ko wace irin matsala ta rashin tsaro a kasar nan, idan har akwai isassun kayan aiki.” A cewarsa.

Har wa yau, DIG ya roki gwamnatin tarayya da ta bar ‘yan sanda su jagoranci yaki da ta’addanci da kuma hare-haren ‘yan bindiga a kasar nan.

Da yake godiya wurin shugabanni da ‘yan kungiyar ta Miyetti Allah kan irin goyon bayan da suke ba jami’an yan sanda. Mataimakin sufeton ya ce: “ Yanzu tsarin aiki ya canza, ba yan sanda ne kadai za suyi wannan aikin ba zamu hada da wasu daga cikin al’umominku.”

A na shi jawabin kuwa, shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Sokoto, Muhammadu Magaji, kokawa yayi kan irin kisan da ‘yan sakai ke yiwa jama’arsu nab a gaira ba dalili. Kana kuma yayi kira ga hukumar ‘yan sanda da ta yi kokarin dakatar da wannan abu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel