Zan yi ritaya daga kwallo qafa bayan AFCON 2019 – Mikel Obi

Zan yi ritaya daga kwallo qafa bayan AFCON 2019 – Mikel Obi

-Dan wasan tsakiya na Najeriya ya ce ya na sa ran ajiye bugawa kasarsa kwallon qafa da zarar an kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka na shekarar 2019 a qasar Masar

-Mikel Obi ya kwashe tsawon shekaru 14 tare da kungiyar kwallon qafa ta Najeriya yana taka leda inda ya samu nasarar bugawa a gasar cin kofin duniya guda biyu

Dan wasa mai rike da kambu na tawagar yan kwallon qafan Najeriya wato Mikel Obi ya ce ya na sa ran yin ritaya daga bugawa qasarsa kwallo da zarar an kammala gasar cin kofin Nahiyar Afirka na shekarar nan a qasar Masar.

Tsohon dan wasan tsakiyan Chelsea ya fara bugawa Najeriya kwallo ne a matakin kasa da kasa a karo na farko ranar 17 ga watan Agusta, 2005. Kawo wa yanzu ya samu nasarar taka leda a gasar cin kofin duniya har guda biyu, inda kuma ya kwashe tsawon shekaru 14 tare da tawagar kallon qafar.

KU KARANTA:Buhari, Masari da makomar APC a Kastina

Da yake magana kan wasan dake gabansu inda zasu fafata da kasar Burundi, dan wasan ya ce: “ Ina da yaqinin cewa zamu bada mamaki a wanna gasar musamman idan akayi la’akari da kokarin da mukayi a baya.”

“ Zuwan mu na karshe wannan qasar ta Masar mune muka lashe kofi. Sai dai kuma bayan wannan nasara da muka samu, mun gagara dawo wa gasar na dan lokaci. Muna da ‘yan wasa masu kokari kwarai da gaske saboda haka nasan zamuyi abin kirki.” Inji Obi.

Da aka tambayeshi kuwa kan yaushe zai yi ritaya daga bugawa kasar wasa cewa yayi: “ To, ajiye kwallon a karshen gasar Masar ba zai zamo laifi ba. A qasar nan na fara buga wannan gasa a shekarar 2006 inda muka zo na 3. A wannan karon kuwa ina da yaqinin cewa zamu zarce kokarinmu na wancan lokacin,bani da tabbas amma wannan kan iya kasancewa gasa ta karshe a gareni.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng