Amfanin ganyen Delbejiya (Dogon yaro) wajen adana hatsi

Amfanin ganyen Delbejiya (Dogon yaro) wajen adana hatsi

-Fidelis Ozuor, darakta a ma'aikatar gona ta jihar Enugu ya bayyana cewa ganyen Bedi na magance kwari a cikin hatsi

-Daraktan ya kara da cewa ya kamata manoma su san yadda ake amfani da busasshen ganyen Bedi wajen adana hatsi

-Haka zalika yayi kira ga manoma dasu guji yin amfani da magungunan kwari saboda suna da illa ga lafiyar dan adam.

Wani masanin aikin gona ya shawarci da a rinka yin amfani da ganyen iccen Bedi wanda akafi sani da ‘Dogon Yaro’ wajen adana hatsi don magance matsalar kwari da tsutsotsi.

Fidelis Ozuor, darakta a ma’aikatar aikin gona ta jihar Enugu ne ya bada wannan shawarar a lokacin da yake zanawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Enugu.

Ozuor ya ce da a rinka yin amfani da magungunan kwari da suke da hadari wajen adana hatsi, to kwara a cakuda hatsin da busasshen ganyen bedi saboda hakan zai kori kwarin daga zuwa inda hatsin ya ke.

Ya kara da cewa busasshen ganyen Bedi idan aka cakudashi da hasi, to zaiyi aiki kamar maganin kwari wajen adana kayen hatsin.

KARANTA WANNAN: Buhari ya gana da Ganduje, Sanwo-Olu da wasu Gwamnoni a fadar Shugaban kasa

“Ya kamata manoma su san cewa idan aka cakudashi da hasi, to zaiyi aiki kamar maganin kwari wajen adana kayen hatsini. Ana amfani da ganyen bedi wajen adana hatsi saboda ganyen na tsotse danshi daga hatsin.”

“Amfani da busasshen ganyen bedi ita ce hanya mafi sauki, idan ganyen suka bushe baki daya, to sai ka cakudasu da hatsin sa’annan ka kai rumbunka wanda yake a tsaftace kuma iska baya shiga.”

Yayi kira ga manoma dasu guji yin amfani da maganin kwari ya kuma bukace su da suyi amfani da hanya ta gargajiya wajen adana hatsinsu.

Ya ce amfani da ganyen bedi wajen adana hatsi na sanyawa ayi wata da watanni ba tare da kwari sun tunkari hatsin ba.

Daraktan ya bayyana cewa mafi yawancin magungunan kwari da manoma ke mafani dasu na da illa sosai ga lafiyar dan adama. (NAN)

Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twittwe:http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng