Noma tushen arziki: Gwamnatin Kaduna ta bada tallafi na musamman ga manoma masara

Noma tushen arziki: Gwamnatin Kaduna ta bada tallafi na musamman ga manoma masara

-Gwamnatin jihar Kaduna ta bada tallafin iri mai inganci ga manoman masara a jihar domin bunkasa harkokin noma a Kaduna.

-Daraktan hukumar cigaban harkokin noman Kaduna mai kula da yankin Maigana ne ya bada wannan sanarwa a ofishin hukumar dake Sabon garin Zaria.

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayar da tallafin ingantaccen iri da yawansa ya kai kilo 5000 ga manoman masara domin bunkasa harkokin noman jihar.

Daraktan hukumar cigaban harkokin noman jihar Kaduna mai kula da yankin Maigana, Alhaji Ahmad Abubakar ne ya bada wannan sanarwa a ofishin hukumar dake Sabon garin Zaria.

KU KARANTA:An daura auren diyan sanata Ida Ibrahim da Almakura yau Asabar

Abubakar ya roki manoma da suyi amfani da irin ta hanyar da ya dace domin samun damar cin moriyarsa.

Daraktan ya ce: “ Kamfanin Value Seed ne ya bai wa gwamnan Kaduna Mallam Nasiru Ahmad El-Rufai kyautar irin domin habbaka harkokin noman jihar Kaduna.”

“ Wannan abu da kamfanin yayi, ya farantan ran mai girma gwamnan musamman duba ga cewa manoma ne zasu amfana da wannan ingantaccen iri.”

Abubakar ya cigaba da cewa: “ Yankin Maigana ya samu kilo 1,700 wanda zai wadaci eka 85 ta filin noma, bayan kuwa an kammala noma anyi girbi muna tsammanin buhu 3,400 na masara.”

“ Dukkanin kananan hukumomin dake yankin Maigana zasu amfana da wannan sabon iri na masara da aka bada.”

Bugu da kari, “ Hukumar mu na cigaba da gudanar da wasu muhimman shirye-shirye guda biyu domin bunkasa ayyukan noma a jihar Kaduna. Manoman da suka samu horo daga wurin malaman gona wanda gwamnati ta sa aikine kawai zasu amfana da wannan sabon tsari.” A cewar Abubakar. (Kamfanin dillacin labarai na kasa, NAN).

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel