Dan jarida da jami’an gwamnati sun tsallake rijiya da baya a Zamfara

Dan jarida da jami’an gwamnati sun tsallake rijiya da baya a Zamfara

-Jami'an hukumar bayar da taimakon gaggawa ta NEMA a jihar Zamfara sun tsallake tarkon yan baranda a kan hanyarsu ta zuwa Kanoma domin rabon kayayyakin tallafi ga yan sansanin gudun hijira.

-Daga cikin tawagar da su kayi nasarar kubuta daga masu garkwar akwai jami'an hukumar bayar da agajin gaggawan jihar Zamfara da kuma wakilin jaridar The Nation a Zamfara.

Babban sakataren hukumar bayar da taimakon gaggawa ta jihar Zamfara (ZEMA), Eng. Sanusi Muhammad Kwatarkwashi, wakilin jaridar The Nation a Zamfara, Sani Muhammad Sani da jami’an hukumar bayar da taimakon gaggawa ta kasa (NEMA) sun tsallake tarkon masu garkuwa da mutane a karshen makon nan.

Rahotanni sun nuna cewa jami’an na kan hanyarsu ne ta zuwa Kanoma dake karamar hukumar Maru domin raba kayayyakin tallafi a sansanin yan gudun hijira dake yankin.

KU KARANTA:An daura auren diyan sanata Ida Ibrahim da Almakura yau Asabar

Ba tare da sanin wadannan jami’an ba, ashe masu garkuwa da mutane sun dana tarko a daidai hanyar dake sadarwa zuwa cikin garin Kanoma inda motar dake dauke da tallafin ta riga ta iso a wannan lokacin.

Kwatarkwashi ya ce: “ An sanar da ‘yan barandan labarin zuwanmu bayan da mota mai dauke da kayan tallafin ta riga mu isa wurin.”

Daraktan rabon kayayyakin tallafin na ZEMA, Alhaji Aminu Muhammad Anka shi ne ya fara hango yan baradan tun yana kimanin mita 15 tsakaninsu rike da miyagun makamai.

“Kimanin mutum biyar daga cikinsu labe suke a bayan bishiya, yayin da sauran kuwa sukayi basaja tamkar ma’aikatan sintiri dake kula da wurin.” A cewar Aminu.

Ba tare da bata lokaci ba motar dake dauke da jami’an ta juya domin komawa inda ta fito. Sai ga wani mai babur nan ya nufo su da niyyar tsayar dasu inda yake cewa ai mafarauta ne ba miyagun mutane bane.

Kwatarkwashi ya cigaba da cewa: “ Hakan bai sa mun tsaya muka bar wajen a guje saboda nasan Zamfara bata da mafarauta kuma yankin Kanoma na daya daga cikin garuruwan da su kayi kaurin suna wurin yawan ‘yan baranda.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel