An daura auren diyan sanata Ida Ibrahim da Almakura yau Asabar

An daura auren diyan sanata Ida Ibrahim da Almakura yau Asabar

-An daura auren Muhammad Ibrahim Ida da Amina Ahmadu Almakura yau Asabar a Lafia babban birnin jihar Nasarawa.

-Bikin ya samu halartar manya-manyan mutane da dama wadanda suka fito daga sassa daban-daban na kasar nan.

Dan gidan sanata Ibrahim Ida na jihar Katsina da diyar sarkin Kwandare Alhaji Ahmadu Almakura babban wa ga sanata Umaru Almakura sun angwance ranar Asabar a wani kayataccen biki.

Babban limanin masallacin Gabas dake Kwandare, Sheikh Abdullahi Liman ne ya daura wannan aure tsakanin Muhammadu Ibrahim Idda da amaryarsa Amina Ahmadu Almakura.

KU KARANTA:Lauyan kare hakkin bil adama ya maka gwamnatin tarayya kara kotu

Yayin da yake kulla wannan aure, limamin ya shawarci ma’auratan da suka kasance abokan juna domin zamansu ya daure har karshen rayuwarsu.

Mataimakin gwamnan Nasarawa Dakta Emmanuel Akabe ne ya wakilci gwamna Abdullahi Sule a wurin bikin.

Sarkin Lafia, Jastis Sidi Dauda Bage (mai ritaya) ne ya bada auren Amina yayin da Dan-madamin Katsina Alhaji Sada Usman Usman Nagogo ya karba wa angon aurenta a madadin sarkin Katsina Dakta Abdulmumini Kabir Usman.

Zamu iya tunawa a ranar 23 ga watan Afirilu ne Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman ya aika da tawagar mutum 25 domin a nema wa Muhammadu auren Amina wurin gwamnan jihar Nasarawa a wancan lokacin sanata Umaru Tanko Almakura.

Bikin ya samu halartar manyan mutane daga sassan daban-daban na kasar nan.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel