Yan APC 3 ke harin kujerar kakakin majalisar Bauchi

Yan APC 3 ke harin kujerar kakakin majalisar Bauchi

-Majalisar dokokin jihar Bauchi na shirye-shirye zaben sabon kakakin majalisa ta tara a ranar Litinin, inda za'a fafata tsakanin yan jam'iyar APC uku ciki hadda tsohon kakakin majalisa ta takwas.

-Jam'iyar PDP wacce ita ke mulkin jihar Bauchi na goyon bayan Abubakar Suleiman, dan majalisa mai wakiltar gundumar Ningi.

Yayin da majalisar dokokin jihar Bauchi ke shirin zaben sabbin shugabanni wadanda zasu ja akalar majalisar ta 9, yan jam’iyar APC 3 ne ke harin kujerar kakakin majalisar.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa akwai rikicin rashin sanin ko daga wane yankin jihar ne da sabon kakakin majalisar zai fito.

KU KARANTA:Kungiyar Igbo ta roki Buhari ya nada sakataren tarayya daga bangarensu

Har ila yau, jam’iyar PDP mai mulkin jihar nada rawar da zata iya takawa wurin zaben wanda zai kasance kakakin majalisar.

Bugu da kari, jam’iyar PDP bata da rinjaye a majalisar inda take da mambobi 8, APC ita ce mafi rinjaye da mambobi 22 inda jam’iyar NNPP ke da mutum daya kacal.

Haka zalika, jam’iyar PDP ta bayyana goyon bayanta zuwa ga daya daga cikin yan takarar mai suna Abubakar Suleiman wanda yake sabo ne a majalisar kuma yana wakiltar gundumar Ningi.

Sauran yan takarar biyu su ne: tsohon kakakin majalisar Kawuwa Shehu Damina wanda ke wakiltar gundumar Darazo da Tijjani Muhammad Aliyu, shugaban masu rinjaye na majalisar wanda ke wakiltar gundumar Azare/Mangala.

Wata majiya wacce keda masaniya game da yadda tsarin karba-karba ke tafiya a majalisar ta shaida mana cewa, “ jam’iyar PDP ba zata iya goyon bayan tsohon kakakin majalisar ba saboda alakarsa da gwamnatin da ta wuce.”

Majiyar ta cigaba da cewa: “ Jam’iyar PDP na son kakakin yazo daga yankin Bauchi ta tsakiya amma dai kada ya kasance wanda za’a zabar ya fito daga karamar hukumar Darazo.”

Sai dai kuma majiyar The Nation ta samu labarin cewa tsohon kakakin yana so yayi amfani da karfin iko da yake dashi saboda da dama daga cikin mambobin zasu sake dawo majalisar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel