Gwamnan Gombe yayi nadin sabbin mukamai biyu

Gwamnan Gombe yayi nadin sabbin mukamai biyu

- Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na Gombe yayi nadin mukamai biyu a ranar Alhamis

- Ya bai wa Abubakar Ibrahim Njodi, sakataren gwamnatin jihar sai kuma Bappayo Yahaya shugaban ma'aikata na jihar

- Da yake rantsar da su gawamnan ya nemi su kasance masu zagewa a fagen aiki domin kawo ma jiharsu ta Gombe cigaba

A jiya Alhamis ne gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya rantsar da Farfesa Abubakar Ibrahim Njodi a matsayin sakataren gwamnatin jihar da kuma Alhaji Bappayo Yahaya a matsayin shugaban ma’aikatan jihar.

Gwamnan ya nemi wdannan mutane da su kasance masu jajircewa da kuma kishin jihar tasu yayin gudanar da aikin da ya rataya a kawunansu.

KU KARANTA:Mafi karancin albashi: Gwamnonin PDP sun shirya biyan N30,000

A wani labari mai kama da wannan kuwa, mun ji cewa kotu ta bada umarni ga hukumar zabe mai zaman kanta cewa lallai ta ba tsohon gwamnan Imo Rochas Okorocha shahadar cin zabe.

Wannan umarnin yazo ne ana daf da kaddamar da sabuwar majalisar dokoki wanda zai kasance ranar Talata 11 ga watan Yuni, 2019.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel